Ni ba makiyin addinin Musulunci bane - Wike

Ni ba makiyin addinin Musulunci bane - Wike

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi kira ga masu sukarsa kan labarin cewa ya rusa Masallacin Trans-Amadi, su tabbatar da sihhancin labari kafin magana a kai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda shugaban kungiyar gwamnoni kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya kai ziyara Masallacin.

A wani jawabi da yayi kama da tafka da warwara, Wike ya bayyana cewa shi ba makiyin addinin Musulunci ko wani addini bane.

Yace: "Ba ni wata kiyayya ga addinin Musulunci ko wani addini saboda kamar yadda kake gani, babu wani Masallaci a nan gurin, juji ne, kuma an kasance ana sa'insa tsakanin wasu mutane da gwamnati kan filin."

KU KARANTA: Za'a tafi da Zakzaky kasar Malaysiya ko Indonisiya jinya

A makonnin, gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyanawa duniya cewa jihar Rivers ta mabiya addinin Kirista ce.

A faifain bidiyon, an ga inda gwamna Wike ke furuci a wurare daban-daban akalla guda uku inda yake jaddada cewa ba ya shakkan fadawa kowa cewa jihar Rivers da yake shugabanta ta mabiya addini daya ce.

Bayan haka, tsohon gwamnan jihar Kano, kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, ya caccaki gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, kan rusa Masallacin da yayi a birnin Port Harcourt.

Ya siffanta wannan abu a matsayin shirme da abin takaici.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel