Kuma dai! Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 6 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Kuma dai! Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 6 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Wasu mutane yan gari daya da suka fito daga garin Offa na jahar Kwara sun fada hannun gungun yan bindiga masu garkuwa da mutane dake tare hanyar Abuja zuwa Kaduna sun satar mutane, inj rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin kungiyar yan asalin garin Offa, Offa Descendant’s Union (O.D.U) Maruf Ajenifuja ne ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 8 ga watan Satumba, inda yace mutanen suna hanyar zuwa Kaduna ne a cikin motar kamfanin sufuri ta Aduke Okin.

KU KARANTA: Direbobin haya sun koka da dawowar masu garkuwa da mutane kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

“Wannan lamari mai tayar da hankali ya faru ne a daidai kauyen Rijana, a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, wanda a yanzu haka lamarin ya jefa jama’a cikin alhini da tashin hankali.

“A yanzu dai kungiyar (O.D.U) ta shiga cikin maganan, kuma muna ta bakin kokarinmu don ganin an sakosu, muna sa rai da ikon Allah za su fito nan bada jimawa ba, ba zamu iya baku cikakken jawabi ba saboda lamari ne na tsaro.” Inji shi.

Ko a ranar Asabar sai da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da wani hafsan Soja mai mukaman Laftanar a garin Zaria ta jahar Kaduna, yayin da ya tafi wani shago da nufin yin saye saye, kamar yadda kaakakin Yansandan Kaduna, Sabo Yakubu Ya tabbatar.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin da ta gabata, inda yan bindigan suka tasa keyar Sojan mai suna Laftanar A. Falana, wanda a lokacin da lamarin ya auku baya sanye da kayan Sojoji.

Sai dai kaakaki Sabo yace: “Mun samu labarin cewa a wani shago dake kusa da jami’ar Ahmadu Bello aka yi awon gaba dashi da yammacin ranar Litinin, amma rahotanni sun tabbatar da cewa ya tsira da ransa.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel