Za'a tafi da Zakzaky kasar Malaysiya ko Indonisiya jinya

Za'a tafi da Zakzaky kasar Malaysiya ko Indonisiya jinya

Da yiwuwan na ba da dadewa ba, za'a sake fitar da shugaban kungiyar mabiya kungiyar IMN da aka fi sani da Shi'a, kasar Maaysiya ko Indonisiya domin cigaban jinyarsa, The Nation ta bada rahoto.

Kakakin kungiyar yan Shi'an, Ibrahim Musa, ya bayyanawa manema labarai cewa tabbas za'a fita da su amma bai san tabbacin kasar da zasu zaba ba.

Yace: "Na san ya ce za su duba wasu kasashe daban - Malaysiya ko Indosiya. Ban sani ko sun yanke shawara ba akan haka."

Hakazalika, Musa ya jaddada cewa yan Shi'a za su gudanar da muzaharar Ashura gobe a Abuj ada wasu jihohin tarayya duk da umurnin da sifeto janar na hukumar yan sanda yayi na damkesu.

KU KARANTA: Kotu ta kwace kujerar Sanata Manager, ta bayar da umurnin sake sabon zabe

A bangare guda, Mabiya akidar Shi'a a jihar Sokoto sun lashi takobin cigaba da ayyukansu duk da cewa gwamnatin tarayya ta haramta kungiyar ta IMN.

Shugaban kungiyar na jihar Sokoto, Malam Sidi Manniru, ya bayyanawa manema labarai cewa umurnin da sifeto janar na hukumar yan sandan tarayya, IG Muhammad Adamu, yayi na rusa dukkan matattaran yan Shi'a da shugabanninsu barazanace kawai.

A cewarsa, babu irin barazanar da zai sanya su rabuwa da kungiyarsu.

Manniru yace: "Mun san abinda sukeyi, biyayya ce ga kasashen waje irinsu Saudiyya, Amurka da Isra'ila amma ba zasu samu nasara ba."

"Ba zaku iya kashe kungiya ta hanyar damkemu ko rusa cibiyoyinmu ba saboda ba su muke bauta ba, Mu Allah muke bauta kuma kundin tsarin mulkin Najeriya ta amincewa kowani dan kasa ya bautawa abinda yake so ko da kyandir ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel