Bidiyon Lai: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kujerar mulki

Bidiyon Lai: PDP ta nemi Buhari ya sauka daga kujerar mulki

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sauka daga kujerar mulki akan wani bidiyo da ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed yayi, inda ya roki yan Najeriya da su yafe ma Buhari akan zarginsa da satifiket din WAEC na karya.

PDP tayi korafi cewa bidiyon daidai yake da amsa laifinsa da kuma wani yunkuri na bayar da hakuri da son zuciya, ganin cewa Shugaban kasar ya gaza kare kansa a gaban kotun zaben Shugaban kasa.

Jam’iyyar tace ba abune mai muhimmanci ba cewa ko an kirkiri bidiyon ne ko kuma ministan yayi jawabin ne a 2015, kamar yadda aka yi ikirari.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a ranar Lahadi, 8 ga watan Satumba, a Abuja, babban sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Kola Ologbodiyan, yace an baza bidiyon ne ga duniya domin “ya taba zuciyar kotun zaben ta yadda zata bi doka bayan a gabatar mata da kwakkwaran hujja a gabanta” kan shugaba Buhari.

KU KARANTA KUMA: Atiku da Buhari: Kotun zabe na shirin yanke hukunci a wannan makon

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya roki 'yan Najeriya su yafewa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan batar da takardun makarantarsa na sakandare da yayi.

Ministan kuma jigo na jam'iyyar APC ya bayar da hakurin ne a wani bidiyo da ya bayyana, a lokacin da yayi wata hira da gidan talabijin na Channels Tv, jiya Juma'a 6 ga watan Satumbar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel