Mahara sun kashe mutane 2 a jihar Filato

Mahara sun kashe mutane 2 a jihar Filato

Mun samu cewa rayukan mutane biyu sun salwanta a yayin da mutane biyar suka jikkata biyo bayan wani mummunan harin 'yan bindiga da ya auku a daren ranar Lahadin da ta gabata cikin kauyen Nding na gundumar Fan a karamar hukumar Barikin Ladi ta jihar Filato.

Kamar yadda mashaida wannan mugun ji da mugun gani suka bayyana, mummunan harin da ya auku da misalin karfe 7.00 na Yammaci na zuwa ne bayan 'yan kwanaki kadan da aukuwar makamancin sa a gundumar Foron, inda rayukan mutane uku suka salwanta gami da satar shanu da dabbobin kiwo fiye da dari biyu.

Sanata mai wakilcin mazabar Filato ta Arewa a majalisar dattawa, Istifanus Gyang, yayin zantawa da manema labarai na jaridar Vanguard cikin birnin Jos a ranar Litinin, ya bayyana takaicinsa da kuma yin Allah wadai da wannan ta'addanci.

KARANTA KUMA: Neman a zauna lafiya ya sa Jonathan bai hukunta Buhari ba kan haifar da rikici a babban zaben kasa na 2011 - Adoke

Sanata Gyang wanda ya kasance mataimakin shugaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa, ya misalta wannan hare-hare da aka kai mazabarsa da abin Allah wadai.

A wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Munanan hare-hare sun ci gaba da aukuwa a fadin Najeriya inda a makon da ya gabata rayukan mutane 17 suka salwanta yayin da mutane bakwai suka afka tarkon masu garkuwa da neman kudin fansa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel