Neman a zauna lafiya ya sa Jonathan bai hukunta Buhari ba kan haifar da rikici a babban zaben kasa na 2011 - Adoke

Neman a zauna lafiya ya sa Jonathan bai hukunta Buhari ba kan haifar da rikici a babban zaben kasa na 2011 - Adoke

Daga karshe gaskiya ta bayyana, dangane da dalilai da suka sanya tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan, bai hukunta Janar Muhammadu Buhari ba, wanda a wancan lokaci ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar CPC duk da haifar da rikicin da yayi a fadin kasar nan, wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama bayan babban zaben kasa na 2011.

Cikin wani sabon littafi da ya wallafa a kan nauye-nauyen da suka rataya a kan tsaffin lauyoyin koli na Najeriya, tsohon lauyan koli kuma ministan shari'a na Najeriya, Muhammad Adoke, ya bayyana dalilai da suka sanya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kwana lafiya bayan haifar da tarzoma a kasar nan da ta salwantar da rayukan mutane da dama a zaben kasa na 2011.

Tsohon ministan shari'ar kasar ya ce, neman a zauna lafiya ya sanya Buhari bai fuskanaci wani hukunci ba duk da haifar da rikicin da yayi bayan babban zaben kasa na 2011, wanda yayi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama ciki har da wasu masu yi wa kasa hidima guda 12.

Adoke cikin sabon littafinsa da ya wallafa, ya ce yanayin kasar a wancan lokaci ya sanya gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ta sauya ra'ayi inda ta fasa cafke Buhari tare da hukunta shi, domin kuwa a cewarta aiwatar da sabanin hakan zai iya kara jefa kasar nan cikin rudani da tashin-tashina.

Tsohon lauyan koli na kasa ya ce, muradin kwantar da tarzoma da neman a zauna lafiya ya sanya gwamnatin tsohon shugaban kasa Jonathan ta fita batun Buhari ba tare hukunta shi ba. Ya ce hakan ya bayu ne a sanadiyar wani kwamitin bincike da hangen nesa da gwamnatin ta kafa bisa jagorancin fitaccen jagoran addinin Islama na Arewacin Najeriya, Sheikh Ahmed Lemu.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki

A wani rahoto da jaridar BBC Hausa ta ruwaito, hukumomin kasar Najeriya sun mayar da zazzafan martani ga kalaman tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, wanda yace; zaben da za'a yi a shekarar 2011 zai iya zama barazana ga zaman lafiyar a kasar.

A wata sanarwa da Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta bayyana cewa; kalaman Mista Campbell na nuni da irin mugun fatan da tsohon jakadan ke yiwa Najeriya.

Sanarwar wadda ke dauke da sa hannun tsohon Ministan ma'aikatar wato Mista Odien Ajumogobia ta bayyana cewa, kalaman sun kasance abin takaici, ganin yadda Mista Campbell ke yunkurin rura wutar tashin hankali a kasar, sabanin magabatansa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel