Yan daba sun tarwatsa zaben fidda gwani na karamar hukuma, an kasha mutum 1, an raunata wasu 5

Yan daba sun tarwatsa zaben fidda gwani na karamar hukuma, an kasha mutum 1, an raunata wasu 5

Rahotanni sun kawo cewa mutum daya ya rasa ransa yayinda yan daba suka kai hari ga wani jami’in zabe a ranar Lahadi, 9 ga watan Satumba, akan bayyana Mista Abdullahi Suleiman Chukuba a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na shugaban karamar hukuma, a yankin karamar hukumar dake Shiriro a jihar Neja.

Chukuba yayi takara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kwamishinan yan sandan jihar, Alhaji Adamu Usman ne ya bayar da sanarwan a wani jawabi da yayi ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Minna.

Ya bayyana cewa sauran mutane biyar sun ji rauni a lokacin harin.

Ya bayyana cewa DPO din yan sanda na yankin da sauran hukumomin tsaro sun kubutar da jami’in zaben daga cibiyar hada kuri’u zuwa Minna.

Ya bayyana cewa bayan sanar da sakamakon zaben , wassu mutane masu biyayya ga dan takaran da ya sha kayi, Alhaji Akilu Isiyaku, sun kai hari ga jami’in zaben inda suka fasa mishi mota.

KU KARANTA KUMA: Atiku da Buhari: Kotun zabe na shirin yanke hukunci a wannan makon

Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar reshen jihar, zata yi iya bakin kokarinta don ganin ta an hukunta wadanda ke da hannu a cikin lamari.

Shugaban yan sandan yayi gargadin cewa za’a kama duk wani ko kungiya da aka kama da laifi za’a kuma hukunta su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel