Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki

Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki

A yau Litinin 9 ga watan Satumban 2019, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinabjo, ya jagoranci zaman majalisar kula da tattalin arzikin a cikin fadar Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Osinbajo yayin jagorantar zaman majalisar tattalin arziki

Osinbajo yayin jagorantar zaman majalisar tattalin arziki
Source: Twitter

Osinbajo, ministocin Buhari yayin zaman majalisar tattalin arziki

Osinbajo, ministocin Buhari yayin zaman majalisar tattalin arziki
Source: Twitter

Osinbajo, ministocin Buhari da kuma masu ruwa da tsaki a yayin zaman majalisar kula da tattalin arziki

Osinbajo, ministocin Buhari da kuma masu ruwa da tsaki a yayin zaman majalisar kula da tattalin arziki
Source: Twitter

KARANAR KUMA: Rayuka 17 sun halaka, an yi garkuwa da mutane 7 a fadin Najeriya cikin makon jiya

Wadanda suka halarci zaman sun hadar da ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Shamsuna Ahmed, ministan masana'antu, kasuwanci da hannun jari, Mr Adeniyi Adebayo da kuma mai ba shugaba kasa shawara a kan tattalin arziki, Dr Adeyemi Dipeolu.

Kamar yadda mataimakin shugaban kasar ya bayyana a shafinsa na Twitter, ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba za ta gushe ba wajen ci gaba da aiki tukuru domin inganta jin dadin rayuwarsu.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel