Rayuka 17 sun halaka, an yi garkuwa da mutane 7 a fadin Najeriya cikin makon jiya

Rayuka 17 sun halaka, an yi garkuwa da mutane 7 a fadin Najeriya cikin makon jiya

Munanan hare-hare sun ci gaba da aukuwa a fadin Najeriya inda a makon da ya gabata rayukan mutane 17 suka salwanta yayin da mutane bakwai suka afka tarkon masu garkuwa da mutane kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

A daya daga cikin munanan hare-haren da suka auku, mayakan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram, sun kai wa wata tawagar sojoji hari na kwanton bauna inda suka yi awon gaba da naira miliyan 15.5 da aka tanada domin dakaru da ke ci gaba da fafatawa da 'yan ta'adda a filin daga.

Kazalika 'yan Boko Haram sun bude wuta a kan tawagar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

Hukumar 'yan sandan jihar Ondo a ranar Litinin, ta tabbatar da salwantar rai guda a yayin wata sa'insa da ta auku a tsakanin wani mutum, Adetutu Ibrahim, da kuma wasu mata a layin Oke Ogba cikin birnin Akure.

Kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar, Ebere Amaraizu ya zayyana, wasu 'yan bindiga sun yi gakuwa da shugaban matasa na jam'iyyar PDP, Ude Okoye. Sai dai an sanar da kubutar sa bayan sa'o'i 24.

A ranar Talata cikin jihar Jigawa da ke Arewacin Najeriya, Hajiya Ladi Hamza, mahaifiyar tsohon hadimi na musamman a kan harkokin siyasa a gwamnan jihar, Muhammad Badaru, ta afka tarkon masu garkuwa da mutane.

A yayin wani hari na ramuwar gayya dangane da munanan hare-haren kin jin baki da ake yi mazauna kasar Afirka ta Kudu, hukumar 'yan sandan Najeriya ta harbe wani matashi daura da shagon Shoprite a jihar Legas.

An kashe mutum guda yayin da mutane da dama suka jikkata a sanadiyar barkewar wani rikici na makiyaya da manoma da ya auku cikin karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa a ranar Laraba.

KARANTA KUMA: Ni zan sake lashe zaben gwamnan jihar Kogi - Yahaya Bello

A daren ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne wasu mayakan Boko Haram, suka bude wuta a kan tawagar gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yayin da ya ke kan hanyarsa ta dawowa daga ziyarar aiki da ya kai karamar hukumar Bama. Sai dai babu rai ko daya da ya salwanta.

A rahoton dai da jaridar Premium Times ta ruwaito, wani farfesan nazarin lissafi na jami'ar kimiya da fasaha ta jihar Ondo, Gideon Okedayo, ya afka tarkon masu garkuwa da mutane

Haka kuma a ranar Asabar cikin kauyen Vatt na gundumar Foron a jihar Filato, 'yan bindiga yayin sabunta hare-hare, sun sheke wasu mutane biyu, Musa Gwom da John Bulus.

A daren ranar Asabar din da ta gabata ne 'yan bindiga suka salwantar da rayukan mutane goma, inda daga bisani hukumar 'yan sandan jihar ta bayar da tabbaci a kan adadin rayuka takwas da suka salwanta.

Harin ya auku ne a kauyen Mgbo na karamar hukumar Ohaukwu, bayan da wasu mutane hudu a yankin suka afka tarkon masu garkuwa da mutane.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel