Ni zan sake lashe zaben gwamnan jihar Kogi - Yahaya Bello

Ni zan sake lashe zaben gwamnan jihar Kogi - Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya kaddamar da cewa ya kammala duk wasu shirye-shirye domin tabbatar da nasararsa yayin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba na 2019.

Furucin gwamnan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya gabatar yayin zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kadan bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari da kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole.

Duk da cewar ba zai saki jiki ba a yanzu, gwamna Bello ya ce ya kammala duk wasu shirye-shirye na tabbatar da nasararsa tun gabanin babban zaben kasa na shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar tarayya da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata.

A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, gwamna Bello ya ce kwazo gami da rawar da ya taka a bisa kujerar mulki manuniya ce ta nasara domin kuwa ya zuwa yanzu al'ummar Kogi sun shirya tsaf domin sake kada masu ruwan kuri'u a zaben jihar na watan jibi.

KARANTA KUMA: An kama 'yan gargagiya 9 da suka kai hari wuraren ibada a jihar Ogun

A yayin jaddada kudirin gudanar da zabe na gaskiya da adalci, ya kuma hikaito kwazon da yayi a bisa kujerar da rawar da ya taka wajen bunkasa ci gaba a jihar, musamman biyan albashin ma'aikata a kan kari da kuma ingancin tsaro, lamarin da ya ce aminci ya wadata a jihar.

Kazalika gwamnan ya bayyana yadda ya magance kalubale na basussukan albashi da ma'aikatan jihar suka fuskanta a karkashin jagorancin gwamnoni biyu da suka shude na jam'iyyar adawa ta PDP.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel