Atiku da Buhari: Kotun zabe na shirin yanke hukunci a wannan makon

Atiku da Buhari: Kotun zabe na shirin yanke hukunci a wannan makon

Kotun zabe shugaba kasa za ta yake hukuci akan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar suka shigar inda suke kalubalatar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban kwamitin mutum biyar, Justiis Mohammed Garba yayinda yake jinginar da hukunci a ranar 21 ga watan Agusta, ya bayyana cewa za a sanar da dukkanin bangarorin da abun ya shafa ranar yanke hukunci.

Kotun zaben bata sannya ranar yanke hukunci ba amma wa’adin da dokar ta dibarwa karar zai kare a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba. Hakazalika sashi na 134 (2) da (3) na dokar zaben 2010, ya dibarwa karar zabe wa’adin kwanaki 180 ne domin kammaluwa.

A nashi bangaren, lauyan INEC, Yunus Ustaz Usman (SAN) yace hukumar ta gudanar da zaben ranar 23 ga watan Fabrairu daidai da dokar zaben sannan cewa masu karar ba za su taba chanja hakan ba.

Don haka ya bukaci kwamitin da yayi watsi da karar wanda bai da fa’ida.

Har ila yau, lauyan Buhari, Wole Olanipekun (SAN) ya bukaci kotun zabe da ta yi watsi da karar akan rashin hujja, inda ya kara da cewa sashi na 131 naa kudi tsari mulki ajeriya bai bukaci a sanya satifiket ciki takardun ba.

KU KARANTA KUMA: APC da PDP: 'Yan siyasar arewa 6 dake rike da manyan mukamai duk da ana tuhumarsu da laifin cin hanci

Lauya APC, Lateef Fagbemi (SAN), yace PDP da Atiku wadada suka zargi magudi zabe a rumfuna 119,973 a yankuna 8,809 da ke kananan hukumomi 774, sun kira shaidu 62 ne kawai wanda daga ciki biyar ne kadai suka jagoranci hujja daga rumfunar zabe.

Sai dai kuma lauyan PDP da Atiku, Levy Uzoukwu (SAN) yya bukaci kotun zaben da ta riki cewa sashi 138(1) na dokar zabe, yace duk dan takarar da ya gabatar da bayanni karya za a soke takararsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel