APC da PDP: 'Yan siyasar arewa 6 dake rike da manyan mukamai duk da ana tuhumarsu da laifin cin hanci

APC da PDP: 'Yan siyasar arewa 6 dake rike da manyan mukamai duk da ana tuhumarsu da laifin cin hanci

Har yanzu hukumomin yaki da cin hanci da rasha wa da karya tattalin arziki na cigaba da tuhumar wasu 'yan siyasa daga dukkan sassan Najeriya duk da an zabe su ko kuma an nada su a mukaman siyasa. Daga cikin irin wadannan 'yan siyasa akwai gwamnoni, sanatoci da mambobin majalisar dattijai.

Ga jerin wasu fitattun 'yan siyasa 6 daga yankin arewa dake fuskantar tuhumar laifin cin hanci a gaban kotu amma kuma yanzu suna rike da manyan mukaman siyasa;

1. Bala Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi a karkashin jam'iyyar PDP, Bala Mohammed, na fuskantar tuhuma guda shidda a gaban kotu dake da alaka da bayar da bayanan karya yayin cike takardun bayyana kadarori da kuma badakalar kudi da yawansu ya kai miliyan N864 a lokacin da yake rike da mukamin ministan Abuja daga shekarar 2010 zuwa 2015.

2. Gabriel Suswan

Tsohon gwamnan jihar Benuwe, Gabriel Suswan, wanda yanzu shine sanata mai wakiltar jihar Benuwe ta gabas a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, yana fuskantar tuhuma kala uku, kowacce mai zaman kan ta, a gaban kotu.

Suswan na fuskantar tuhumar karkatar da kudin jihar Benuwe da yawansu ya kai biliyan N3.1 lokacin da ya yake gwamna daga shekarar 2007 zuwa 2015. Kazalika, ana tuhumarsa da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba. An samu tsohon gwamna Suswan da karamar bindiga guda daya, wata karamar bindiga mai karfin harbi da kuma wata babbar bindiga samfurin AK47.

Suswan na fuskantar wasu tuhuma 32 masu nasaba da karkatar da rarar kudaden cire tallafin man fetur da aka bawa jihar Benuwe lokacin da yake gwamna.

3. Sanata Dino Melaye

Sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma a jam'iyyar PDP, Dino Melaye, na fuskantar tuhuma a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja da kuma wata babbar kotun jihar Kogi dake Lokoja bisa zarginsa da laifin garkuwa da mutane, kokarin hana jami'an tsaro gudanar da aikinsu da kuma safarar bindigu.

Rundunar 'yan sanda ta gurfanar da Dino Melaye bisa zarginsa da yunkurin kashe kansa domin saka rundunar 'yan sanda cikin halin 'ni 'ya su'.

4. Aliyu Wammako

Tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma sanatan APC mai wakiltar arewacin jihar Sokoto a yanzu, Wammako na fuskantar tuhumar satar kudin jama'a da kuma karkatar da biliyan N15 mallakar gwamnatin Sokoto lokacin da yake gwamnan jihar daga shekarar 2007 zuwa 2015. A shekarar 2015 ne hukumar EFCC ta bayyana cewa ta fara binciken zargin da ake yi wa Wammako na karkatar da adadin kudaden.

5. Abba Moro

Tsohon ministan harkokin cikin gida, yanzu kuma sanata mai wakiltar kudancin jihar Benuwe a jam'iyyar PDP, Abba Moro, na fuskantar tuhumar tafka almundahana da sunan daukan aiki a hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar matasa masu neman aiki su 20 a shekarar 2014.

6. Abdullahi Adamu

Tsohon gwamnan jihar Nasarawa, kuma sanata mai wakiltar yammacin jihar a karkashin inuwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, tare da wasu mutane 18, na fuskantar zargin tafka almubazzaranci da biliyan N15 lokacin da yake gwamnan jihar Nasarawa daga 1999 zuwa 2007.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel