JNI ta wanke Gwamna Wike kan tsige Shugaban hukumar Alhazan Ribas

JNI ta wanke Gwamna Wike kan tsige Shugaban hukumar Alhazan Ribas

Mun samu labari daga jaridar nan jaridar Sahara Reporters cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom C. Wike ya sallami shugaban hukumar nan da ke kula da Alhazai ta jiharsa daga aiki.

Idan ba ku manta ba. hakan na zuwa ne bayan gwamnan ya yi ikirarin cewa jihar Ribas ta Kiristoci ce kwanakin baya. Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce da surutun jama’a daga fadin kasar.

Sai dai wani mataimakin shugaban hukumar Jamaatu Nasril Islam, (JNI), Abubakar Orlu, ya bayyana abin da ya sa gwamna Nyesom Wike ya dauki wannan mataki mai tsauri.

Alhaji Abubakar Orlu ya ke cewa gwamnan ya sauke shugaban hukumar Alhazan ne a dalilin wasu badakala da ke faruwa a hukumar a lokacin da ya ke rike da ofis a jihar Ribas.

KU KARANTA: Abin da ya sa Buhari ba ya daukar mataki kan masu sukarsa

Kamar yadda mu ka ji, Jagoran na hukumar JNI watau Jamaatu Nasril Islam, ya na cewa, a baya a kan karbe wasu kujerun aikin Hajji a jihar Ribas a mikawa wasu jihohin Najeriya.

Abubakar Orlu wanda ya yi magana a madadin JNI ya fito ya yi wannan jawabi ne Ranar Asabar, 7 ga Watan Satumba, 2019 a daidai wannan lokaci da jama’a su ka yi ca a kan Wike.

A watan Yuli ne gwamna Wike ya fito ya na nanata cewa Jihar Ribas ta Kiristoci ce. Bayan nan kuma gwamnatinsa ta rusa ginin wani masallacin Juma’a da ke cikin Garin Fatakwal.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel