Zaben 2019: Mun yi safarar bindigu da makamai ga manyan 'yan siyasa a jihohin arewa uku - Dillalin bindigu

Zaben 2019: Mun yi safarar bindigu da makamai ga manyan 'yan siyasa a jihohin arewa uku - Dillalin bindigu

Dakarun rundunar atisayen 'Whirl Stroke' (OPWS) dake aikin tabbatar da tsaro a jihohin Benuwe, Nasarawa da Taraba sun kama wasu masu laifi 19 a sassa daban-daban na jihohin bisa aikata laifukan da suka hada da garkuwa da mutane da safarar miyagun makamai.

Da yake bajakolin masu laifin ranar Asabar a sansanin rundunar sojin sama (NAF) dake Makurdi, kwamandan rundunar OPWS, manjo janar Adeyemi Yekini, ya ce sn kama 13 daga cikin masu laifin a Gboko da Katsina-Ala na jihar Benuwe.

Yekini ya nuna Dauda Atara da Andrew Imbwase a matsayin manyan masu safarar miyagun makamai ga kasurgumin dan ta'adda da ake nema a ruwa a jallo, Terwase Akwaza (wanda aka fi kira da 'Gana').

Da yake magana da manema labarai, Andrew Imbwase, mai safarar makamai, ya ce an kama shi ne saboda safarar bindigu.

"An bani kwangilar safarar makamai 2000 ga wani dan siyasa a Gboko, na samu kwangilar ne ta hannun abokina, Dauda Atara. Na samu makaman ne ta hannun wani mutum a karamar hukumar Shendam dake yankin jihar Filato.

DUBA WANNAN: 'Yan Boko Haram sun kai wa tawagar sojoji hari, sun kwaci kudi fiye da miliyan N15 da muhimman kayayyaki

"Na san Gana (kasurgumin dan ta'adda) kuma na sha yi masa safarar makamai kafin daga bisani na aikata wani laifi da ya jawo aka rufe ni a gidan yari.

"An fito da ni daga gidan yari gabanin babban zaben 2019 domin na taimaki wasu 'yan siyasa. Na karbi bindigu samfurin AK47 guda uku da alburusai masu yawa daga wurin Dauda, wannda na yi amfani da su lokacin zabe," a cewarsa.

Kazalika, shi ma Dauda ya amsa cewar shine ke safarar bindigu ga Gana da Imbwase (wanda aka fi kira da 'Don Moji')

"Duk abinda Don Moji ya fada gaskiya ne, nine ke yi masa safarar bindigu da alburusai. Ba AK47 uku muka yi safara ga 'yan siyasa ba, guda hudu ne kuma tun shekarar 2014 nake yi wa Gana safarar bindigu," a cewar Dauda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel