Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wadanda suka yi garkuwa da dan majalisa, daliban ABU a Kaduna

Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wadanda suka yi garkuwa da dan majalisa, daliban ABU a Kaduna

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta sanar da kama wadanda suka yi garkuwa da mamba a majalisar dokokin jihar Kaduna, Sulaiman Dabo.

Kazalika, rundunar 'yan sandan ta sanar da kama wadanda suka yi garkuwa da daliban jami'ar ABU, Zaria.

A daren ranar juma'a ne kafafen yada labarai suka sanar da sace dan majalisar a Kaduna. An sake shi sa'o'i kadan da sace shi bayan an biya kudin fansa.

Su ma daliban jami'ar ABU an sake su ne bayan biyan kudin fansa.

Rundunar 'yan sandan ta sanar da kama masu laifin ne a yammacin ranar Lahadi, ta bakin kakakinta na jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo.

Masu laifin na daga cikin masu garkuwa da mutane 25 da rundunar 'yan sandan ta sanar da cewa ta kama yayin atisaye daban-daban a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna da kuma Kaduna zuwa Zaria.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya sanar da hakan ne a cikin wani jawabi da ya fitar da yammacin ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: An tsinci gawar dan sanda ta fara rube wa a jeji sati uku bayan sace shi

A cewar Sabo, wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen da aka kama ne suka amsa cewa sune suka yi garkuwa da dan majalisar mai wakiltar mazabar Zaria da kuma daliban.

A cikin jawabin da Sabo ya fitar, ya bayyana cewar jami'an rundunar atisayen 'Puff Adder' ne suka kama 'yan ta'addar a wata maboyarsu dake kauyen Kingimi a yankin karamar hukumar Igabi a ranar 6 ga watan Satumba.

"Yayin da ake tuhumarsu ne aka gano cewa sune masu garkuwa da mutane da suka addabi hanyar Kaduna - Abuja da Kaduna - Zaria.

"Bincike mai zurfi ya gano cewa masu garkuwa da mutanen, karkashin shugabansu, Buhari Bello, mai shekaru 34, sune suka sace mamba a majalisar dokokin jihar Kaduna, Sulaiman Dabo," a cewar Sabo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel