An tsinci gawar dan sanda ta fara rube wa a jeji sati uku bayan sace shi

An tsinci gawar dan sanda ta fara rube wa a jeji sati uku bayan sace shi

An samu gawar wani jami'in dan sanda ta fara rube wa a wani jeji dake jihar Ribas ranar Alhamis da ta gabata.

Wasu 'yan bindiga ne suka sace jami'in dan sandan, Saja Lawrence Igbero, wanda ke aiki da rundunar PMF (Police Mobile Force) a kan hanyar zuwa Ogoni a jihar Ribas.

Tun bayan sace Saja Igbero, kwamamdan rundunar rundunar da yake aiki, Egbe Sunday, yasa aka yi wa jejin yankin kawanya amma ba a iya samun shi ba.

Daga baya ne jami'an 'yan sandan suka gano wayarsa ta hannu a wurin wani mutum, wanda ya yi ikirarin cewa sayenta ya yi.

Ta hannun mutumin da ya sayi wayar ne 'yan sanda suka kama wanda ya sayar masa da ita.

Bayan wanda ya sayar wa da mutumin wayar ya sha matsa a hannun 'yan sandan ne ya fadi cewa sun kashe saja Igbero kuma sun jefar da gawarsa a cikin jeji.

Binciken jami'an 'yan sandan ya gano cewa 'yan ta'addan da suka kashe saja Igbero na da hannu a aiyukan ta'addanci da suka hada da garkuwa da mutane da fashin ababen hawa a yankin Ogoni.

Majiyar 'yan sanda ta bayyana cewa sun gane gawar saja Igbero saboda akwai kakinsa na aiki a jikinsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an ajiye gawar jami'in a dakin ajiyar gawa domin gudanar da bincike.

Kazalika, ya bayyana cewa an kama mutum guda dangane da kisan dan sandan, kuma har yanzu yana tsare yayin da ake cigaba da gudanar da bincike a kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel