Dattijo dan shekara 137 ya mutu bayan sauke duk wani bashi a jihar Zamfara

Dattijo dan shekara 137 ya mutu bayan sauke duk wani bashi a jihar Zamfara

A halin yanzu al'ummar Mareri ta karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara, na ci gaba da makokin mutuwar wani dattijo mai shekaru 137 a duniya, Malam Isah Mareri, wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar.

Malam Mareri wanda ya rasu ya bar kimanin jikoki da tattaba kunne 200, ajali ya katse masa hanzari bayan fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya.

Daya daga cikin jikokin marigayi Malam Mareri, Alhaji Labaran wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar 'yan tireda a birnin Gusua, ya ce rasuwar kakansa ta jefa dukkanin al'ummar Mareri cikin jimami bayan da suka samu rahoton mai yankar kauna ta yi abin da aka santa a akai.

Da yake zayyana takaicin wannan babban rashi, Alhaji Labaran ya ce mutuwar kakansa ta bar wani wawakeken gurbi da babu wanda zai iya cike shi, lamarin da ya ce za su yi kewarsa musamman kyawawan akidu da ya dabi'antu da su a yayin rayuwarsa.

Manema labarai na jaridar Tribune sun ziyarci yankin Mareri domin daukan rahoto a sanadiyar yadda manyan mutane, hamshakan 'yan kasuwa da kuma manyan 'yan siyasa ke tururuwa wajen gabatar da ta'aziyyar su duk da rashin kyawun hanya.

KARANTA KUMA: Kin jinin baki: Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi magana kan ziyarar da Buhari zai kai a watan gobe

Manema labaran sun bayyana damuwa dangane da yadda yankin na Mareri duk da kasancewarsa cikin birnin Gusau tsawon shekaru aru-aru, ya gaza sharbar romon dimokuradiya a sanadiyar rashin samun wadatacciyar hanya, ruwan sha, ballantana asibiti.

Wani daga jikokinsa yayin zantawa da manema labarai, Mallam Siddi, ya bayar da shaidar yadda marigayi Mallam Mareri ya yi kyakkyawar rayuwa inda gabanin mutuwarsa ya tabbatar da sauke nauyin duk wani bashi dake kansa ciki har da wata N20 da ya biya daya daga cikin jikokin sa.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel