Kin jinin baki: Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi magana kan ziyarar da Buhari zai kai a watan gobe

Kin jinin baki: Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi magana kan ziyarar da Buhari zai kai a watan gobe

- Har yanzu akwai kyakkyawar alaka a tsakanin mu da Najeriya inji kasar Afirka ta Kudu

- Afirka ta Kudu ta jadadda kudirinta na magance rikicin kin jinin baki da ya mamaye kasar

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Afirka ta Kudu a watan Oktoba

A yayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara kasar Afirka ta Kudu a watan gobe na Oktoba, gwamnatin kasar ta ce har yanzu akwai kyakkyawar alaka da ke tsakanin kasashen biyu.

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi wannan furuci ne domin jaddada kudirin ta na magance rikicin kin jin baki da a baya-bayan nan yayi sanadiyar kai wa 'yan Najeriya mazauna can munanan hare-hare.

Fadar gwamnatin Afirka ta Kudu cikin wata sanarwa ta bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar a watan Oktoba na 2019 domin jaddada kyakkyawar dangartaka da ke tsakanin kasashen biyu tare da hadin kai wajen magance rikicin da ke kalubalantar al'ummomin kasashen biyu da kuma sana'o'insu.

Biyo bayan munanan hare-hare na kin jinin baki musamman 'yan Najeriya mazauna kasar Afirka ta Kudu, shugaban kasar Cyril Ramaphosa a birnin Pretoria, ya gudanar da wata ganawa a ranar Juma'a 6 ga watan Agusta, tare da jakada na musamman na Najeriya, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar, wanda gwamnatin kasar nan ta bai wa wakilcin tunkarar barazanar da tunkaro kasar a baya-bayan nan.

KARANTA KUMA: Ganduje ya samu kyautar gwamnan da ya fi kowanne kwazo a Najeriya bayan hawa kujerar mulki da kwanaki 100

Ana iya tuna cewa, shugaba Buhari ya yi wata ganawa ta daban tare da shugaban kasar Afirka ta Kudu yayin da shugabannin biyu suka halarci taron bunkasa nahiyyar Afirka da aka gudanar a garin Yokohama na birnin Tokyo a kasar Japan.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel