Ganduje ya samu kyautar gwamnan da ya fi kowanne kwazo a Najeriya bayan hawa kujerar mulki da kwanaki 100

Ganduje ya samu kyautar gwamnan da ya fi kowanne kwazo a Najeriya bayan hawa kujerar mulki da kwanaki 100

Bayan kwanaki 100 na farko a bisa kujerar mulki, wata cibiyar dimokuradiyya ta Afirka mai tushe a birnin Dakar na kasar Senegal, ta zabi gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin gwamnan da ya fi kowanne kwazo a halin yanzu a Najeriya.

Cibiyar mai akidar dimokuradiyya ta ADAN, African Democracy Assessment Network, ta ayyana gwamna Ganduje a matsayin gwamnan da ya yi wa sauran gwamnonin Najeriya fintinkau ta fuskar kwazo a bisa kujerar mulki, lamarin da ta ce ya cancanci kyauta ta musamman.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, wannan sanarwa ta ranar Lahadi na kushe ne cikin wata rubutacciyar wasika da sa hannun babban sakataren yada labarai na fadar gwamnatin Kano, Abba Anwar.

Duba da bincike gami da nazari da cibiyar ADAN ta yi a kan gwamnonin Najeriya kamar yadda babban jami'in ta na reshen Afirka ta Yamma, Samson Theodore ya bayyana, ta ce babu shakka gwamnan Kano ya ciri tutar kwazo bayan kwanaki 100 kacal da hawa kujerar mulki.

ADAN ta yi kididdiga a kan gwamnonin Najeriya duba da rawar da kowanensu ya taka a wasu muhimman bangarori na bunkasa ci gaban al'umma.

KARANTA KUMA: Mulkin kama karya a siyasar Kano ya sanya na fice daga masana'antar Kannywood - Naburiska

Baya ga tasirin jam'iyyar siyasa a jihohin da kowane gwamna ya kasance a kai, ADAN ta yi kididdigar ta a fannin ilimi, lafiya, noma, tsaro, tattalin arziki da kuma bunkasar ci gaban gine-gine a kowace jiha.

A wasikar da ADAN ta aike da ita zuwa fadar gwamnatin Kano, ta yabawa kwazon Ganduje musamman a kan akidarsa da kuma tsare-tsaren da ya bullo da su na wajabta neman ilimi ga dukkanin yaran Kano a matakin farko na Firamare da Sakandire.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel