Direbobin haya sun koka da dawowar masu garkuwa da mutane kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Direbobin haya sun koka da dawowar masu garkuwa da mutane kan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Bayan da ta'addancin masu garkuwa da mutane ya sake sabunta tare da munana a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, direbobin haya sun koka dangane da yadda wannan lamari ke tursasa wa suna kauracewa sana'ar su.

Babu shakka dimuwa da tashin hankali sun dabaibaye hanyar Kaduna zuwa Abuja a yayin da ta'addancin masu garkuwa ya sabunta.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, kashe-kashe da da ta'adar gakuwa da mutane tare da neman kudin fansa ta munana, lamarin da ya jefa dubban direbobin haya cikin halin ni ‘ya su sanadiyar lamarin da ke haramta masu hanyar neman abinci.

A kwanan baya ne masu ta'adar garkuwa suka hallaka mutane uku tare da cafke mutane da dama ciki har da wasu daliban jami'ar ABU uku, sai dai daga bisani an sanar da rahoton kubutar su bayan da iyayensu suka biya kudin fansa.

Wadanda ta'addancin masu garkuwa da mutane ya fi jefawa cikin tsaka mai wuya a yanzu sune direbobin haya masu bibiyar hanyar Kaduna zuwa Abuja, a sanadiyar yadda lamarin ke sanya wa suna tserewa daga sana'arsu ta neman abinci.

KARANTA KUMA: Akwai yiwuwar za a yi arangama tsakanin 'yan shi'a da 'yan sanda a ranar Talata

Shugaban tashar motoci ta jihar Kaduna, Emmanuel Ameh, yayin zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, ya ce ‘yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Abuja na kai hare-hare tare da yin garkuwa da mutane a kullum babu dare babu rana.

Ameh ya hikaito yadda ya tsira daga afkawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane daura da wata gada a kauyen Rijana da misalin karfe 8:00 na dare.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel