Ban bada umarni a cafke Rochas Okorocha ba – Inji Gwamna Ihedioha

Ban bada umarni a cafke Rochas Okorocha ba – Inji Gwamna Ihedioha

Gwamna Emeka Ihedioha na jihar Imo, ya karyata rahotannin da ke yawo a gari cewa ya bada umarni a kama tsohon gwamna kuma Sanatan jihar Imo a yanzu watau Owelle Rochas Okorocha.

Mai girma gwamna Ihedioha ya fitar da wani jawabi ta hannun babban Sakatarensa na yada labarai, Chibuike Onyeukwu, a Ranar Asabar 8 ga Watan Satumba, 2019, inda ya karyata jita-jitar.

A cewar wannan jawabi da gwamnan ya yi, karya ne kurum aka shirga na cewa ya sa a damke tsohon gwamnan. Emeka Ihedioha ya ce zai cigaba da bin dokar kasa a matsayinsa na gwamna.

Ihedioha ya ke cewa ba zai shiga tsoma kansa a cikin binciken da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta ke yi game da Okorocha ba. Gwamnan dai ya na mai cewa:

“A matsayin mu na gwamnati, mu na sane da labaran kiyayyar da ake dasawa a kan gwamna Emeka Ihedioha, ban da sharrin cewa ya sa a kama tsohon gwamnan jiha, Cif Rochas Okorocha.”

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai zai san makomar sa a kan mulki a makon nan

“Babu karyar da ta fi wannan. Gwamna ya shafe rayuwarsa a majalisar wakilai a matsayin shugaba, wanda aka sani da bin dokar kasa da girmama sauran bangarorin gwamnati.” Inji Onyeukwu.

Chibuike Onyeukwu ya kara da cewa: “A game da zargin laifuffukan tsohon gwamnan wanda hukuma ta ke bincike, Gwamna Emeka Ihedioha ya yi amanna cewa dole a bar doka ta yi halinta”

Jawabin gwamnan ya ce: “Mu na so mu kara tabbatar da cewa, gwamna ba zai shiga cikin binciken tsohon gwamnan da hukuma ta ke yi ba. Za mu cigaba da bin tsarin damukaradiyya.”

Gwamnan mai-ci ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ba za ta aikata wani abu da ya sabawa doka ba. Yanzu dai EFCC sun taso tsohon gwamnan na APC a gaba da Iyalinsa ana kan bincikensu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel