Zaben Kogi: Dino Melaye da Ibrahim sun kai korafi a kan tsaida Wada

Zaben Kogi: Dino Melaye da Ibrahim sun kai korafi a kan tsaida Wada

Wani sabon rikici ya barkowa jam’iyyar hamayya ta PDP a Najeriya a dalilin tsaida Injiniya Musa Wada aka yi a matsayin ‘dan takarar jam’iyyar na zaben jihar Kogi da a za ayi a Nuwamban 2019.

Daily Trust ta rahoto cewa ba Musa Wada tikitin gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a jihar Kogi ya jawo wasu daga cikin ‘yan takarar babbar jam’iyyar adawar sun fara nuna rashin jin dadinsu.

Sanatan PDP na Kogi ta Yamma, Dino Melaye da kuma Abubakar Ibrahim watau ‘Dan tsohon gwamna Ibrahim Idris sun kai kara har gaban uwar jam’iyya a sakamakon nasarar Musa Wada.

Majiya mai karfi daga Hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza a babban birnin tarayya Abuja sun nuna cewa wadannan ‘yan takara da zaben na jihar Kogi ya yi wa zafi, sun kai korafi.

Manyan ‘yan takarar biyu sun gabatar da kararsu gaban majalisar NWC na jam’iyyar ta PDP a geme da yadda aka gudanar da zaben na tsaida gwani a Lokoja Ranar 3 da 4 ga Watan Satumba.

KU KARANTA: 'Dan takarar APC ya sha kaye a kotun zaben Jihar Delta

Abubakar Ibrahim ya samu kuri’u 710 a zaben yayin da Sanata Dino Melaye ya tashi da kuri’u 70 rak. Dino Melaye ya nuna cewa sam bai yarda da zaben ba domin an tafka magudi na inna-naha.

Melaye ya sheka gaban Sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Ibrahim Tsauri, inda ya gabatar da kokensa a jiya 7 ga Watan Satumba, 2019. Ba mu da labari game da matakin da za a dauka.

Shi kuma Ibrahim ya zauna da manyan jam’iyyar a Abuja a daidai lokacin. Tsohon gwamna Idris Wada shi ne ya zo na uku a zaben, amma bai nuna alamun cewa bai yi na’am da sakamakon ba.

‘Dan takarar PDP wanda zai kara da gwamna Yahaya Bello watau Musa Wada ya kawo ziyara zuwa ofishin jam’iyyar tare da dinbin Mabiyarsa. PDP tace za ta duba kukan ‘Ya ‘yan na ta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel