Kotu ta kwace kujerar Sanata Manager, ta bayar da umurnin sake sabon zabe

Kotu ta kwace kujerar Sanata Manager, ta bayar da umurnin sake sabon zabe

- A ranar Asabar ne kotun sauraron kararrakin zabe da ke Asaba ta kwace kujerar James Manager na jam'iyyar PDP

- Mai shari'a O.O Onyeaba ya bada umarnin cewa a kara yin zabe nan da kwanaki 90

- Tsohon Gwamna Emmanuel Uduaghan na jam'iyyar APC ne ya kai koken magudin zaben da aka tafka a jihar

A ranar Asabar, kotun sauraron kararrakin zabe da ke Asaba ta soke zaben James Manager na jam'iyyar PDP.

Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito cewa shugaban alkalan kotun, Mai shari'a O.O Onyeabo ya yanke hukunci kara yin zabe nan da kwanaki 90.

Tsohon Gwamna Emmanuel Uduaghan na jam'iyyar APC ne ya mika kokensa ga kotun domin ta soke nasarar Manager na jam'iyyar PDP.

A karar da Uduaghan ya mika ga kotun, ya zargi cewa akwai magudi mai yawa da jam'iyyar PDP da kuma hukumar zabe mai zaman kanta.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace babban soja a Zaria

Mai shari'a Onyeabo ya ba wa hukumar zabe mai zaman kanta umarnin karbar shaidar komawa majalisar tarayya ga Manager.

Kotun ta ce ba ta ce wadanda aka yi kara sun kasa kare kansu daga zargin magudin zaben.

Karar ta lissafa inda aka samu magudin zaben da Burutu, Bomadi, Patani, Isoko ta arewa, Warri ta kudu maso yamma da Warri ta arewa.

A maida martani da lauyan Manager ya yi, yace wanda ya ke karewa bai gamsu da hukuncin ba.

Ya sanar da manema labarai jim kadan bayan yanke hukuncin cewa zasu kara duba hukuncin kafin daukaka kara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel