A ranar Litinin mai zuwa ne El-Rufai na jihar Kaduna zai san makomarsa

A ranar Litinin mai zuwa ne El-Rufai na jihar Kaduna zai san makomarsa

- A ranar Litinin mai zuwa ne Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna zai san makomarsa

- Ranar ne kotun sauraron kararrakin zabe zata yanke hukuncin shari'ar da ta gudanar a ranar 19 ga watan Augusta

- Jam'iyyar PDP da Dan takararta, Isah Ashiru ne suka shigar da karar sakamakon zargin da suka yi na magudin zabe a zaben 9 ga watan Maris

A ranar Litinin mai zuwa, 9 ga watan Satumba ne za a yanke hukunci akan karar da aka shigar ta kara zaben Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna.

Sakatariyar kotun sauraron kararrakin zabe, Hafsat Suleiman, ta bayyana hakan ga manema labarai a ranar asabar a garin Kaduna.

Suleiman tace kotun sauraron kararrakin zaben ta kammala zamanta ne a ranar 19 ga watan Augusta kuma ta sa ranar Litinin a matsayin ranar da zata fidda hukuncinta akan karar da jam'iyyar PDP ta shigar.

Jam'iyyar PDP da Dan takararta, Isah Ashiru, sun shigar da kara akan zaben ranar 9 ga watan Maris tare da bukatar kotun ta soke zaben.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace babban soja a Zaria

Karar ta bukaci kotun da ta soke kuri'u 515,951 wadanda jam'iyyar ta ce anyi aringizonsu ne.

Masu karar sun gabatar da shaidu 135 a cikin shaidu 685 da suka ce suna da su kuma sun zargi magudi a wajen zaben.

Masu karar sun kara da zargar hukumar zabe mai zaman kanta da karawa El-Rufai na jam'iyyar APC kuri'u 391,741 da kuma kuri'u 124,210 ga jam'iyyar PDP.

Sun kara da cewa, bayyana El-Rufai a matsayin wanda ya lashe zaben ya karya doka domin ba shi ne ya ci mafi yawan kuri'u ba.

Jam'iyyar PDP ta bakin lauyoyinta wadanda Emmanuel C. Ukala, SAN ya jagoranta, yace rage kuri'u 391,741 daga 1,045,427 na El-Rufai da kuma kara kuri'u 124,210 ga 814,168 na Ashiru zai maida nasara ga jam'iyyar PDP kuma Ashiru zai karbe karagar mulkin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel