Matasa a Kano sun yi zanga-zangar lumana kan hare-haren Afrika ta Kudu

Matasa a Kano sun yi zanga-zangar lumana kan hare-haren Afrika ta Kudu

Wasu matasa a Kano a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, sun gudanar da zanga-zangar lumana akan hare-haren da ake kaiwa yan Najeriya da ke zama a kasar Afrika ta Kudu.

Matasan wadanda suka yi tattaki daga hanyar Zoo Road zuwa sakatariyar Audu Bako, sun kasance dauke da kwalaye da rubutu daban daban inda suka Allah wadai da matakin harin da ake kai wa yan Najeriya.

Masu zanga-zangar, wadanda suka yi kira ga gwamnatin kasar Afrika ta Kudu domin ya kawo karshen wannan hare-hare, sun ayyana cewa ba za su nade hannu suna kallo ba alhalin ana kai wa yan Najeriya hari sannan ana kashe su ba.

Kakakin masu zanga-zangar kuma Shugaban kungiyar hadin gwiwa da ke yaki akan hare-haren da ake kaddamarwa, Khalid Sanusi ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauke matakan gaggawa domin duba mummunan al’amarin.

Sanusi yace matasan za su ci gaba da nuna fushinsu akan iri wannan hare-hare sannan za su mamaye kamfanonin da suke mallakar kasar Afrika ta Kudu a Najeriya, har sai an dauki matakin kawo karshen hare-hare.

KU KARANTA KUMA: Kotun zabe ta tabbatar da dan takarar PDP a matsayin sanatan Delta

Ya daura alhakkin akan yawan rashin aikin a kasar Afrika ta Kudu a matsayin baban dalilin da yasa suke kai hare-haren, sannan ya shawari gawamnatin Afrika ta Kudu da ta magance lamarin.

Duk da haka yace wwannan bai isa yasa su kai hare-haren ba saboda gazawar gwamnatin kasarsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel