Yanzu-yanzu: Jirgi dauke da mahajjata 600 ya samu hadari a jihar Neja

Yanzu-yanzu: Jirgi dauke da mahajjata 600 ya samu hadari a jihar Neja

Jirgin dake dauke da fasinjoji 600 da suka kammala aiki hajjin bana a kasar Saudiyya ya samu hadari yayinda yake kokarin sauka a babban filin jirgin saman Minna, jihar Neja.

Rahoton The Nation ya bayyana cewa jirgin kirar, Boeing 744 mai lamba 5N/ DBK ya samu fuskanci mishkila ne yayinda daya daga cikin injinan jirgin hudu ya samu matsala lokacin da ya isa filin jirgin saman.

Wani majiya a filin jirgin saman da ya tabbatarwa manema labarai wannan labari ya ce babu wanda ya rasa rayuwarsa kuma babu wanda ya raunata amma fa fasinjojin sun girgiza.

An ga alamar hadarin jirgin a wani sashen filin jirgin saman inda ya lalata wasu kayayyaki lokacin da kauce daga hanya.

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta damke yan daba 100 a jihar Kano (Hotuna)

Kakakin hukumar jin dadin alhazan jihar Neja, Hajia Hassana Isah, ta tabbatar da faruwa wannan lamari amma bata bayar da cikakken bayani ba.

Wasu ma'aikatan sashen binciken hadari daga jihar Legas guda biyar sun iso Minna domin duba abinda ya faru inda suka shiga ganawar sirri da manyan jami'an filin jirgin saman.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa Allah ya kiyaye jirgin bai kama da wuta ba saboda babu motocin yan kwana-kwana a filin jirgin saman.

Yace: "Da wutan ya kona filin jirgin saman gaba daya saboda babu motocin yan kwana-kwana a fili jirgin saman."

Har yanzu, hukumomin jirgin saman basu yi magana kan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel