Delta: Kotu ta soke zaben James Manager, ta yi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90

Delta: Kotu ta soke zaben James Manager, ta yi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90

Kotun da ke sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin tarayya da ke zama a Asaba, babbar birnin jihar Delta, a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, ta soke zaben James Manager, dan majalisa mai wakiltan yankin Delta ta Kudu a majalisar dokokin tarayya.

Tsohon gwamnan jihar kuma dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben, Emmanuel Uduaghan, a wata kara da ya shigar ta hannun lauyansa, Thomson Okpoko (SAN), ya fada ma kotun zaben cewa anyi magudi da rashin bin ka’ida a zaben majalsar dokokin tarayyar wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu, sannan ya roki kotun da ya soke zaben sannan tayi umurnin sake sabon zabe.

Da take yanke hukunci, kotun zaben bayan tayi duba ga dukkanin muhawarar da aka tafka a gabanta, ta soke zaben sannan tayi umurnin sake sabon zabe cikin kwanaki 90.

KU KARANTA KUMA: Abinda yasa shugaba Buhari baya daukar mataki akan masu zagin shi a shafukan sadarwa - Gwamnatin tarayya

A wani lamari makamanci haka Legit.ng ta rahoto a baya cewa kotun zaben majalisar dokokin tarayya da na jiha da ke zama Asaba, babbar birnin jihar Delta, a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, ta jaddada zaben Sanata Peter Nwaoboshi a matsayin sanata mai wakiltan yankin Delta ta arewa a majalisar dokokin tarayya.

Kotun zaben, da take yanke hukunci ta yi watsi da karar da Doris Uboh na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar, kan hujjar cewa bai da fa’ida.

Nwaoboshi ya kasance dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben majalisar dokokin tarayya a ranar 23 ga watan Fabrairu, a jihar Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel