Kotun zabe ta tabbatar da dan takarar PDP a matsayin sanatan Delta

Kotun zabe ta tabbatar da dan takarar PDP a matsayin sanatan Delta

Kotun zaben majalisar dokokin tarayya da na jiha da ke zama Asaba, babbar birnin jihar Delta, a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba, ta jaddada zaben Sanata Peter Nwaoboshi a matsayin sanata mai wakiltan yankin Delta ta arewa a majalisar dokokin tarayya.

Kotun zaben, da take yanke hukunci ta yi watsi da karar da Doris Uboh na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar, kan hujjar cewa bai da fa’ida.

Nwaoboshi ya kasance dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben majalisar dokokin tarayya a ranar 23 ga watan Fabrairu, a jihar Delta.

Shugaban kwamitin mutum uku na kotun zabe, Justis E.I. Ngene, a lokacin da yake zartar da hukunci, yace akwai fa’ida akan kalubalantar karar da Sanata Nwaoboshi yayi da kuma cewa kotun zaben bata da hurumin sauraron karar domin an shigar dashi ne a kurarren lokaci da doka ya tanadar.

Koda dai, an soke karar da Uboh ta shigar akan kalubalantar lamarin da Sanata Nwaoboshi yayi da farko, kotun zaben ta sauraro lamarin domin jin fa’idarsa.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama sojan da ya soki wani bawan Allah har lahira

Justis Ngene ya bayyana cewa kotun zaben ta gano cewa mai karar ta gaza tabbatar da ko daya daga cikin zargin magudin zaben a gaban kotu yadda ya kamata.

Uboh wacce ta samu kimanin kuri’u 30,000, ta shigar da kara kotun zabe sannan ta kalubalanci nasarar Nwaoboshi na PDP wanda ya samu kuri’u 180,000 a zaben 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel