Shugaban IPOB fadi dalilan da za su sanya su hana gwamnoni zuwa kasashen ketare

Shugaban IPOB fadi dalilan da za su sanya su hana gwamnoni zuwa kasashen ketare

- Shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu ya ce nan gaba kadan za su hana gwamnoni zuwa kasahen ketare shakatawa

- Ya ce ba za su hari kowa ba, za dai su tsare gwamna ne har sai ya sanar da dalilin hana ma'aikata albashi

- Hukuncin nasu ba wai kan gwamnonin kudu ya tsaya ba, ba za su damu da jiha ba

Shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya hori gwamnonin da ke rike da albashin jama'a da cewa nan ba da dadewa ba za a hanasu zuwa shakatawa turai.

Nnamdi Kanu ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da 'BEN TV London', Kanu ya ce ba za su hari gwamnonin ba sai dai zasu amsa tambayoyi akan dalilan da yasa suke rike albashi da kudin fanshon ma'aikata.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace babban soja a Zaria

A kalamansa, "Nan gaba kadan, duk gwamnan da baya biyan ma'akata albashi zamu hanasa zuwa kasar waje. Idan ana binka albashi, ba ka da damar zuwa kasar waje. Ku biya malaman makaranta albashi kuma ku biya ma'aikatan da suka yi murabus hakkokinsu."

"Yanzu muka fara. Ba zamu hari kowa ba; zamu tsare su ne har sai sun bamu dalilan da suka sa aka ki biyan ma'aikata albashi."

"Duk gwamnan da yaki biyan albashi kuma muka ganshi, zamu tambayeshi me yake da kudin ma'aikata? Dole ne ka yi mana bayani. Ba mu damu daga wacce jiha kake ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel