SUBEB ta gano sunayen malamai 256 matattu da har yanzu suke karbar albashi a Benue

SUBEB ta gano sunayen malamai 256 matattu da har yanzu suke karbar albashi a Benue

- Hukumar SUBEB ta jihar Benue ta gano malaman makaranta 256 matattu da ke karbar albashi a jihar

- Hukumar ta bayyana cewa a shirye take don gyara tsare-tsaren ilimi na jihar

- Hukumar ta kara da jan kunnen sakatarorin kananan hukumomi don tace tana dab da zuwa kansu

Malaman makaranta 256 ne da suka rasu amma suna kan jerin masu karbar albashi a jihar Benue

Shugaban SUBEB na jihar, Mathew Mnyam, ya bayyana hakan a tattaunawar da ya yi da manema labarai a ranar juma'a.

Kamar yadda ya fada, gwamnatin jihar ta fara zakulo ma'aikatan bogi a jihar don kawo gyara ga lamarin ilimi na jihar.

KU KARANTA: Gwamna Ortom na jihar Benue ya bada hakuri ga masu zanga-zanga akan kudin fansho

"Malamai 256 ne suka mutu amma suna kan jerin masu karbar albashi a jihar. Mun kuma cire ma'aikatan da su ka yi murabus daga jerin masu karbar albashin," inji shi.

Shugaban hukumar yace daraktoci uku aka ba wa hutun dole don a samu saukin bincikar lamarin.

Ya kara da cewa an dakatar da daya daga cikin ma'aikatan hukumar SUBEB sakamakon makala wasu sunaye da ya yi a jerin masu karbar albashin.

Mnyam yace hukumar na dab da komawa kan sakatarorin kananan hukumomi. Ya kara da jan kunnen hedimastoci akan karbar kudin iyayen yara kafin basu damar kai yaransu makaranta.

Shugaban ya ja kunne da cewa: "Hukumar ba za ta saurarawa sakatarorin kananan hukumomi da aka kama da laifin rashin aikinsu yadda ya dace. Haka kuma shuwagabannin makarantun firamare masu karbar kudin iyayen yara su shiga hankalinsu don hukumar ba za ta sassauta mu su ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel