Abinda yasa shugaba Buhari baya daukar mataki akan masu zagin shi a shafukan sadarwa - Gwamnatin tarayya

Abinda yasa shugaba Buhari baya daukar mataki akan masu zagin shi a shafukan sadarwa - Gwamnatin tarayya

- Gwamnatin tarayya ta fadi dalilan da yasa shugaba Buhari baya daukar mataki akan masu zagin shi a kafar sadarwa

- Ta bayyana cewa duka masu magana a kafar sadarwa babu abinda suka iya sai surutun banza, kuma ba wani yawa ne da su ba shine yasa gwamnati ba ta damu dasu ba

- Wannan magana dai ta fito daga bakin mai taimakawa shugaban kasa a fannin sadarwa, Femi Adesina

Mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren sadarwa, Femi Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa basa son cin mutunci da ake yi masa a shafukan sadarwa, sannan kuma ya fadi dalilin da yasa shugaban kasar bai dauki mataki ba har yanzu.

Adesina ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da jaridar TheCable, inda yake cewa, yayin da wasu ke ganin cewa shugaban kasar bai damu da masu zagin shi ba, wasu kuma suna ganin cewa lokaci yayi da shugaban kasar zai dawo Janar din shi da aka san shi na shekarar 1984.

Ya ce: "Mutane da yawa suna cewa muna son Janar Muhammadu Buhari, ba ma san wannan shugaban kasar na yanzu, muna son Janar Buhari da muka sani a shekarar 1984 zuwa 1985." Mutane da yawa suna fadar haka, hakan zai nuna muku cewa shugaban kasar yayi sanyi a wannan lokacin."

KU KARANTA: Tashin hankali: Budurwa ta kone wani saurayi kurmus akan ya hanata naira 200 da take bin shi

Adesina ya cigaba da magana akan dalilin da yasa shugaban kasar baya daukar mataki akan masu zagin shi a kafar sadarwa, ya ce: "Kuna tunanin kafar sadarwa ita ce kasar nan? Idan har kuna tunanin haka kunyi babban kuskure. Saboda duk masu magana a kafar sadarwa surutun banza suke yi, shine yasa ma bama kula su.

"Idan baku manta ba a zaben da aka yi na watannin da suka gabata, idan kana bin kafar sadarwa zaka dauka cewa mun riga mun fadi zabe ne. Amma mu mun riga mun san cewa surutun banza ne suke yi, saboda haka idan kuka ji irin wannan surutan na kafar sadarwa ku sani cewa wasu 'yan tsiraru ne suke yi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel