Tashin hankali: Budurwa ta kone wani saurayi kurmus akan ya hanata naira 200 da take bin shi

Tashin hankali: Budurwa ta kone wani saurayi kurmus akan ya hanata naira 200 da take bin shi

- An ruwaito cewa bayan sun jike mutumin da ruwan fetur, sai daya matar ta kyasta ashana ta cilla mishi, inda nan take ya kama da wuta.

- Wani shaida ya bayyana cewa ya san dai daya daga cikin matar tana bin mutumin bashi, sai dai kuma shi bai san abinda ya kawo dayar da ta kunna masa wutar ba

- An bayyana cewa mutumin ya mutu a take a wajen kafin a kawo masa wani dauki

Wata mata ta sanyawa wani mutumi wuta, inda ta kone shi kurmus a jihar Delta, yankin kudancin Najeriya akan bashin naira dari biyu da take bin shi.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Delta ta bayyana cewa ta kama matar da ta sanyawa mutumin wuta. Sai dai daya matar da ta taimaka mata wajen kona mutumin ta gudu, inji kwamishinan 'yan sandan jihar Adeyinka Adeleke.

KU KARANTA: Matasa sun yiwa wani malamin addini dukan tsiya, bayan sun kama shi yana kashe mutane yana tsafi da jininsu

Matashin saurayin wanda aka bayyana sunan shi da Sunday an kone shi a garin Effurun dake karamar hukumar Uwvie, cikin jihar Delta.

Wani shaida ya bayyanawa manema labarai cewa matar da ta zubawa saurayin fetur tana binshi kudi ne, amma kuma shi bai da masaniya akan daya matar da ta kunna masa wutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel