Yan sanda sun kama sojan da ya soki wani bawan Allah har lahira

Yan sanda sun kama sojan da ya soki wani bawan Allah har lahira

Rundunar yan sandan jihar Niger ta kama wani soja, Lance Cpl. Attahiru Jibril, kan zargin soke wani Ali Mohammed har lahira, a kasuwar Lanbatta, yankin karamar hukumar Gurara da ke jihar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Alhaji Adamu Usman, kwamishinan yan sandan jihar Niger, ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), a garin Minna a ranar Asabar, 7 ga watan Satumba.

“Wanda ake zargin ya far ma marigayin sannan ya soke shi da wuka har lahira, biyo bayan wani sabani da ya shiga tsakaninsu a kasuwar,” inji Usman.

Ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba.

“Mun yi nasarar ceto wanda ake zargin daga hannun fusatattun matasa a kasuwar sannan mun sanar da mahukunta na rundunar soji yadda ya kamata,” inji kwamishinan.

Usman yace wanda ake zargin yayi ikirarin cewa an tura shi aiki na musamman a Maiduguri, jihar Borno.

Ya kara da cewa za a gurfanar da Jibril a gaban kotu bayan kammala bincike.

KU KARANTA KUMA:

A wani lamarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa masu garkuwa da mutane sun sace soja mai mukamin 'Lieutenant' yayin da ya tafi wani shago domin yin cefane a garin Zaria da ke jihar Kaduna.

Mutanen da suka shaida sace sojan sun sanar da jaridar Saturday Sun cewa sojan ba a cikin khaki yake ba. Ya je siyayyar kayan abinci ne lokacin da masu garkuwa da mutanen suka bayyana tare da tayar da hankulan mutane.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da cigaban a tattaunawar waya da jaridar Saturday Sun tayi da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel