Masu garkuwa da mutane sun sace babban soja a Zaria

Masu garkuwa da mutane sun sace babban soja a Zaria

- Masu garkuwa da mutane sun sace soja mai mukamin 'Lieutenant'

- Sun sacesa ne yayin da yaje cefane a wani shago kusa da jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria

- Tuni dai sojan ya kubuto ba tare da wani abu ya faru da shi ba

Masu garkuwa da mutane sun sace soja mai mukamin 'Lieutenant' yayin da ya tafi wani shago domin yin cefane a garin Zaria da ke jihar Kaduna.

Mutanen da suka shaida sace sojan sun sanar da jaridar Saturday Sun cewa sojan ba a cikin khaki yake ba. Ya je siyayyar kayan abinci ne lokacin da masu garkuwa da mutanen suka bayyana tare da tayar da hankulan mutane.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sanda jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da cigaban a tattaunawar waya da jaridar Saturday Sun tayi da shi.

Sojan da masu garkuwa da mutane suka sace shi ne Lieutenant A. Falana.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Zamfara ya amince da dawo da malaman makaranta 556 da gwamnatin Yari ta kora

An sacesa ne a yammacin ranar Litinin amma tuni ya kubce daga masu garkuwa da mutanen ba tare da wani abu ya faru da shi ba, kamar yadda 'yan sanda suka fadi.

Kamar yadda Sabo ya sanar, "An sanar da mu cewa an sacesa a yammacin ranar Litinin a wani shago kusa da jami'ar Ahmadu Bello. Amma ya kubuta ba tare da wani abu ya same sa ba."

Amma kuma wata majiya daga rundunar sojin ta musa faruwar lamarin. Ta kuma jaddada cewa hakan bai faru ba.

"Bari in duba, zan kira ku,"

Bayan dubawar ya kira tare da shaidawa cewa babu wanda aka yi garkuwa da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel