An kama wani malamin firamare a jihar Adamawa da ya bai wa dalibar shi maganin bacci yayi mata fyade har ciki ya shiga

An kama wani malamin firamare a jihar Adamawa da ya bai wa dalibar shi maganin bacci yayi mata fyade har ciki ya shiga

- An cafke wani malamin makarantar firamare a jihar Adamawa wanda ya yiwa dalibar shi fyade har ta samu juna biyu

- Malamin ya bayyana cewa ya bawa dalibar maganin bacci ne ta sha kafin yayi lalatar da ita

- Dalibar wacce take a ajin malamin, an bayyana cewa ba ta wuce shekara sha biyu a duniya ba

Wani malamin makarantar firamare a jihar Adamawa ya shiga hannun jami'an tsaro bayan ya yiwa dalibar shi fyade har ta samu ciki.

Malamin mai suna Nathan Yusuf, an bayyana cewa ya bai wa dalibar tashi maganin baccine kafin yayi lalata da ita.

Shugaban rundunar hukumar Civil Defence na jihar Adamawa, Abdullahi Nurudeen, ya ce, "A ranar 2 ga watan Satumba, da misalin karfe 2:30 na rana mun kama Nathan Yusuf, mai shekaru 37, wanda yake malami ne a makarantar firamare ta Gurel, dake kauyen Namtari, cikin karamar hukumar Yola ta Kudu, inda ake zargin shi da yiwa dalibar shi fyade mai kasa da shekaru 14.

KU KARANTA: Tirkashi: An yankewa matar shugaban kasa hukuncin shekaru 58 a gidan yari

"Ya amsa laifin shi, inda ya ce ya bata maganin bacci ne kafin yayi lalatar da ita. Da zarar mun gama gabatar da bincike akan lamarin, zamu mika mai laifin zuwa kotu.

"Muna shawartar iyaye da su dinga sanya ido akan 'ya'yansu, sannan su kai rahoto wajen jami'an tsaro da an samu matsala makamancin haka."

Da yake magana da manema labarai a lokacin da ake binciken shi, Yusuf ya bayyana cewa sharin shaidan ne yasa shi aikata wannan mummunan abu, amma yayi alkawarin kula da jaririn idan yarinyar ta haihu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel