Tashin hankali: An kwantar da dalibin jami'ar Najeriya bayan ya shafe kwanaki 41 babu ci babu sha

Tashin hankali: An kwantar da dalibin jami'ar Najeriya bayan ya shafe kwanaki 41 babu ci babu sha

- An kwantar da wani dalibin jami'ar jihar Abakaliki, mai suna Ikechukwu Oke, bayan ya shafe kwanaki 41 ba ci ba sha

- Dalibin ya bayyana cewa ya dauki wannan azumi ne saboda irin halin matsin rayuwa da iyayen shi suke ciki a wannan lokacin

- Yanzu haka dai wasu bayin Allah sun garzaya da shi asibitin koyarwa na Abakaliki domin duba lafiyar shi

Wani dalibin jami'ar jihar Ebonyi wanda aka bayyana sunan shi da Ikechukwu Oke, an kwantar da shi a asibiti bayan ya shafe kwanaki 41 yana azumi da addu'o'i.

Dalibin wanda yanzu haka yake kwance a asibiti, ya bayyana cewa ya fara wannan azumi ne na kwanaki 41 saboda irin matsalolin da iyayen shi suke ciki a 'yan kwanakin nan.

Christian Nwaokpa ya sanar da jaridar Punch cewa "Dalibin dan kauyen Ebiaji ne dake karamar hukumar Ezza ta arewa. Kuma dama can haka yake irin wannan azumin."

KU KARANTA: Karshen zance: Daga yanzu Adam A Zango zai dinga sakin fina-finansa a yanar gizo (YouTube)

"A zancen da muke yanzu, wasu mutanen kirki sun dauke shi zuwa babban asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Abakaliki."

Wannan rahoto yana zuwa ne bayan wani rahoto da ya dinga yawo jiya dake nuna cewa wani Fasto dan kasar Zambiya ya mutu a ranar da ya kai azumi 20 daga cikin 30 da ya dauki niyyar yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel