Tirkashi: An yankewa matar shugaban kasa hukuncin shekaru 58 a gidan yari

Tirkashi: An yankewa matar shugaban kasa hukuncin shekaru 58 a gidan yari

- An yankewa matar shugaban kasar Honduras, Rosa Elena Bonilla hukuncin shekara 58 a gidan yari

- An yanke mata hukuncin ne bayan kamata da aka yi da laifin damfara da kuma almubazzaranci da kudin al'umma

- Sai dai lauyanta ya bayyana cewa ba ta da laifi, inda ya bayyana cewa za su daukaka kara zuwa kotun koli

An yankewa matar tsohon shugaban kasar Honduras, Rosa Elena Bonilla, hukuncin shekaru 58 a gidan yari, bayan kamata da laifin damfara da kuma yin almubazzaranci da kudin al'umma.

Bonilla mai shekaru 52, wacce take matar tsohon shugaban kasa Portfirio Lobo, an cafketa tun watan Fabrairun shekarar 2018. Sai dai kuma lauyanta ya bayyana cewa bata da laifi kuma za su daukaka kara zuwa kotun koli ta kasar.

Ana zarginta da handame kudi kimanin dala dubu dari bakwai da tamanin ($780,000) a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014. An gurfanar da ita ne bayan ministan shari'a na kasar ya gabatar da bincike akan ta.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kwantar da dalibin jami'ar Najeriya bayan ya shafe kwanaki 41 babu ci babu sha

Bonilla ta yi amfani da kudin wajen biyan kudin magani, sayen gwala-gwalai, biyan kudin makarantar 'ya'yanta da dai sauransu, in ji ministan shari'ar kasar.

Haka kuma kotun ta daure na hannun daman Bonilla, Saul Escobar, a gidan yari na tsawon shekaru 48, bayan shima an kama shi da laifi irin na matar shugaban kasar, kakakin kotun koli Carlos Silva shine ya bayyana hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel