Wani jami'in hukumar yaki da rashawa ta EFCC ya kashe kansa a Benin

Wani jami'in hukumar yaki da rashawa ta EFCC ya kashe kansa a Benin

- Wani jami'in hukumar yaki da rashawa ta EFCC ya kawo karshen rayuwarsa da kansa

- Jami'in mai suna Williams ya kashe kansa ne ta hanyar shan maganin kwari 'Sniper'

- Abokinsa ya gano gawarsa a gidansa sakamakon rashin zuwa wajen aiki da bai yi ba a ranar Alhamis

Jami'in hukumar yaki da rashawa, EFCC, Oyibogare Williams, ya kashe kansa ta hanyar shan maganin kwari mai suna 'Sniper'

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa, an samu gawar Williams ne da misalin karfe 7 na safiyar juma'a a gidansa dake yankin Giwa Amu, kan titin filin jirgi, a Benin babban birnin jihar Edo.

Majiya daga jami'an tsaro ta sanar da cewa daya daga cikin abokan aikin Williams ne ya je dubasa a gidansa sakamakon rashin ganinsa a wajen aiki a ranar Alhamis kuma duk kiran wayarsa da yayi baya dauka.

KU KARANTA: Gwamna Ortom na jihar Benue ya bada hakuri ga masu zanga-zanga akan kudin fansho

Daily Nigerian ta samo cewa, yayin da aka fara binciken sanadiyyar mutuwar Williams, an ga takarda kunshe da rubutu da ke nuna shi ya kashe kansa, sai wasu magunguna da kuma gorar maganin kwari 'Sniper'.

Tuni dai aka mika gawarsa ma'ajiyar gawawwaki da ke Central Hospital don binciko sanadiyyar mutuwarsa.

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Wilson Uwujaren bai samu daukar kira ko bada amsar sakon kar ta kwana da aka tura masa don jin matsayar hukumar akan zancen.

A ranar 20 ga watan Yuni, gwamnatin tarayya ta haramta sayarda maganin kwari 'Sniper' kuma ta umarci a janyesa daga kasuwa da gaggawa sakamakon yawaitar kisan kai da ake da maganin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel