Magana ta kare: A karshe dai gwamnatin tarayya ta bawa 'yan Najeriya hakuri akan takardun makarantar shugaba Buhari

Magana ta kare: A karshe dai gwamnatin tarayya ta bawa 'yan Najeriya hakuri akan takardun makarantar shugaba Buhari

- A karshe dai gwamnatin tarayya ta fito ta bai wa 'yan Najeriya hakuri akan batan takardun makarantar sakandare na shugaba Buhari

- Hakan ya fito daga bakin Ministan Labarai da Al'adu ne, Alhaji Lai Mohammed, inda ya roki 'yan Najeriya su yafewa shugaban kasar akan maganar takardun

- Ya ce yanzu shekara 53 kenan da shugaban kasar ya kammala karatunsa, kuma bai san inda takardun nasa suke ba

Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya roki 'yan Najeriya su yafewa shugaban kasa Muhammadu Buhari akan batar da takardun makarantarsa na sakandare da yayi.

Ministan kuma jigo na jam'iyyar APC ya bayar da hakurin ne a wani bidiyo da ya bayyana, a lokacin da yayi wata hira da gidan talabijin na Channels Tv, jiya Juma'a 6 ga watan Satumbar nan.

KU KARANTA: Dubu ta cika: An kama wata mata a filin jirgi da sabon jariri a cikin jakar kaya

Ya bayar da hakurin ne bayan an yi masa tambaya dangane da takardun makarantar shugaban kasar, sai ya ce:

"Shugaban kasar Najeriya ya cancanci a yafe masa, saboda yanzu shekaru 53 kenan da ya kammala makaranta sakandare, kuma bai ma san inda ya ajiye takardun na shi ba."

Wannan dai ya biyo bayan kace-nacen da ake ta faman yi akan cewa shugaban kasar bai kammala karatunsa na sakandare ba, idan ba a manta ba kuma a makon da ya gabata ne muka kawo muku rahoton yadda tsohon na hannun damar shugaban kasar Buba Galadima ya caccaki shugaban kasar akan cewa bashi da takardun makaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel