Rikakken dan bindiga ya ambaci babban jami’in gwamnatin Taraba a matsayin mai daukan nauyinsa

Rikakken dan bindiga ya ambaci babban jami’in gwamnatin Taraba a matsayin mai daukan nauyinsa

Dakarun Yansanda na musamman dake karkashin umarnin babban sufetan Yansandan Najeriya, IRT, sun samu nasarar kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jahar Taraba mai suna Fuski Angulu, a karamar hukumar Takum.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa Fuski Angulu shine ummul haba’isun karuwar hare haren yan bindiga tare da satar mutane da nufin yin garkuwa dasu da kuma fashi da makami a Takum, Donga da garin Wukari.

KU KARANTA: Babban rashi: Buhari ya yi alhinin mutuwar Robert Mugabe

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansandan IRT sun samu bayanan sirri game da Fuski ne, da haka suka lallaba suka yi awon gaba dashi zuwa babban birnin tarayya Abuja. Sai dai yayin da yake amsa tambayoyi, Fuski ya fallasa sunan guda daga cikin gungunsa mai suna Idi Shaidan mazaunin garin Jalingo.

Haka zalika ya ambaci sunan tsohon mashawarcin gwamnan jahar Taraba Darius Ishaku a kan muradun karni, MDG, Alhaji Salejo Damburan da kuma wani kansila a karamar hukumar Jalingo, Shagari Umar a matsayin masu daukan nauyinsa.

Wannan bayani yasa Yansandan IRT suka sake dira jahar Taraba suka cika hannu da Damburam, Shagari da kuma Sunday Kona, sa’annan suka gudanar da binciken kwakwaf a gidajensu, amma daga bisani sun bada belin Damburam da Shagari, yayin da suka wuce da Idi Shaidan da Sunday Kona zuwa Abuja.

Sai dai Danburam ya musanta zargin hannunsu cikin wasu miyagun ayyuka, amma ya bayyana cewa yana sane da cewa Idi Shaidan na daga cikin wadanda suke addabar gidansa da kamfaninsa a Jalingo domin kuwa ya taba kai kararsa ga shugaban DSS na jahar Taraba da kuma Yansandan SARS.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel