Rundunar yan sandan Plateau ta gurfanar da mutane 26 kan aikata miyagun laifuka

Rundunar yan sandan Plateau ta gurfanar da mutane 26 kan aikata miyagun laifuka

Rundunar yan sandan jihar Plateau ta kama sannan ta gurfanar da mutane 26 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban kama daga samunsu da kudade na jabu, fashi da makami, karban ababen hawa na sata, shiga kungiyar asiri da sauran laifuffuka.

Da yake gurfanar dasua hedkwatar rundunar da ke Jos, kwamishinan yan sandan jihar, CP Isaac Akinmoyede yayi jawabi akan laifuffukan da suka aikata, inda ya kara da cewa za a gurfanar dasu a kotu da zaran bincike ya kammala.

Kwamishinan yan sandan ya kuma bayyana makamai da alburusai da aka samu daga gare su sannan yayi kira ga mutanen jihar da su zamo masu lura musamman a lokacin da a yanzu da ake shiga karshen shekara.

Ya kuma yi alkawarin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kakkabe miyagun ayyuka a jihar.

KU KARANTA KUMA: An gano sunayen malamai 256 da suka mutu cikin wadanda ake biyan albashi a hukumar SUBEB na jihar Benue

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayyana cewa 'yan Najeriya 36 ne aka kama da laifin watanda da kasuwancin 'yan kasar Afirka ta Kudu da sunan maida martani.

Mohammed ya sanar da manema labarai ne a ziyarar da suka kai masa a ofishin hukumar 'yan sanda da ke Ado Ekiti a ranar Alhamis.

Adamu yace Najeriya kasa ce da aka gina da dokoki kuma duk Dan kasar da aka kama da laifin nuna banbanci ga 'yan wata kasa mazauna nan za a kamasa da laifin ta'addanci da rashin kishin kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel