Gwamna Ortom na jihar Benue ya bada hakuri ga masu zanga-zanga akan kudin fansho

Gwamna Ortom na jihar Benue ya bada hakuri ga masu zanga-zanga akan kudin fansho

- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bai wa tsoffin ma'aikatan jihar hakurin hakkokinsu da gwamnatin jihar ta riqe

- Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta gada matsalar ne tun daga gwamnatin da ta gabata

- Gwamnan ya yi alkawarin sakarwa tsoffin ma'aikatan jihar hakkokinsu a cikin sati mai zuwa

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bai wa masu zanga-zanga hakuri sakamakon gazawar gwamnatin na biyansu hakkokinsu.

Gwamna Samuel Ortom ya yi jawabi ga fusatattun ma'aikatan da su ka yi murabus a kofar gidan gwamnatin jihar Benue a jiya.

Gwamna Ortom ya yi bayanin cewa sun gada matsalar ne tun daga gwamnatin da ta gabata amma ya yi alkawarin shawo kan matsalar.

KU KARANTA: Gwamnan jihar Zamfara ya amince da dawo da malaman makaranta 556 da gwamnatin Yari ta kora

Gwamnan ya ce, "A gaskiya gwamnati na ta gada bashin Naira biliyan 17 ta kudin sallamar aikin ma'aikata da kuma kudin fansho har Naira biliyan 34 a 2015 daga gwamnatin da ta gabata."

"Amma a duk lamarin, mun biya Naira biliyan 18 ta fansho kuma mun cigaba da biya, amma ana binmu Naira biliyan 20."

"Ina amfani da wannan damar wajen bai wa iyayenmu mata da maza hakuri domin ba ku cancanci wannan abin ba. Ina matukar bakin ciki kuma na damu da zanga-zangar nan. Nasan da yawanku na shan magani kuma kun cancanci a biyaku kudin fanshonku don biyan bukatunku."

Ya ce wasu sun samu kudinsu kwanaki biyu da suka gabata kuma an kara aminta da sakin Naira miliyan 611 don biyan masu murabus din kudadensu na watan Afirilu da Mayu.

A jawabin shugaban ma'aikatan masu murabus, Peter Kyado ya hori gwamnatin jihar da ta cika alkawarin da ta yi wa tsoffin ma'aikatan don kawo karshen zanga-zangar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel