Buhari ya kulle kofa da Oshiomole da Gwamna Yahaya Bello a Aso Rock

Buhari ya kulle kofa da Oshiomole da Gwamna Yahaya Bello a Aso Rock

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakoncin shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole da gwamnan jahar Kogi, Yahaya Bello inda suka yi wata ganawar sirri a fadar Aso Rock Villa a Abuja.

Rahoton kamfanin dillancin labaru,NAN, ta bayyana cewa jiga jigan na jam’iyyar APC sun isa Villa ne da misalin karfe 3:30 na rana, inda suka zarce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa, kuma suka garkame kofa su uku kadai.

KU KARANTA: Sunayen shuwagabannin kasashen Afirka 15 da aka musu juyin mulki daga 201 zuwa 2019

Majiyar Legit.ng ta ruwaito babu wanda ya san dalilin zuwan gwamnan da shugaban APC ofishin Buhari, amma da yake labarin gizo baya wuce na koki, majiyarmu ta hakaito ziyarar baya rasa nasaba da zaben gwamnan jahar Kogi dake karatowa.

A ranar 29 ga watan Agusta ne Yahaya Bello ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC na takarar gwamnan jahar Kogi bayan ya doke yan takara fiye da biyar, zaben ya gudana ne a garin Lokoja.

Haka zalika majiyar na da yakinin shuwagabannin uku sun tattauna wasu batutuwan da suka shafi yan Najeriya kamar hare haren kyamar bakaken fata a kasar Afirka ta kudu.

Idan za’a tuna a karshen zaman gaggawa da jam’iyyar APC ta gudanar a ranar Alhamis a babban birnin tarayya Abuja game da wannan matsalar ya nemi gwamnatin tarayya ta kwace kamfanonin yan kasuwan Afirka ta kudu dake Najeriya, kamarsu MTN, DSTV da kuma bankin Stanbic.

A wani labari kuma, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, wanda ya rasu a ranar Juma’a yana dan shekara 95 a duniya.

Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Mugabe ne ta bakin kaakakinsa, Mista Femi Adesina, inda ya taya iyalai, yan uwa da abokan arzikin Mugabe jimamin rashin da suka yi, ya kara da cewa Mugabe ne ya jagoranci yakin neman yancin kasar Zimbabwe daga mulkin mallaka na turawan yamma, kuma ya yi yawancin rayuwarsa yana bauta ma yan kasarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel