Soji sun mika shanu 134 da suka kwato daga masu garkuwa da mutane ga gwamnatin jihar Kaduna

Soji sun mika shanu 134 da suka kwato daga masu garkuwa da mutane ga gwamnatin jihar Kaduna

- Rundunar soji ta daya dake Kaduna ta mika dabbobi 134 ga gwamnatin jihar Kaduna

- Shanun dai ana zargin masu garkuwa da mutane dake kan babban titin Kaduna zuwa Abuja ne suka sato su

- An samo dabbobin ne a samamen da jami'an suka kai bayan bayanan sirri da suka samu

A ranar Alhamis ne babban kwamandan runduna ta daya dake Kaduna, Birgediya Janar Jimmy Akpor, ya mika wa gwamnatin jihar Kaduna shanu 134 wadanda ake zargin 'yan bindiga ne suka sace.

Dabbobin da suka kai 134 an mika su ne ga jagoran 'Operation Yaki' mai ritaya, AIG Murtala Abbas a kauyen Kakau da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa, dabbobin sun hada da shanu 120 da tumakai 14 wadanda jimillarsu ya kama 134. An kwatosu ne daga hannun masu garkuwa da mutane da suka addabi titin Kaduna zuwa Abuja.

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kai wa tawagar Gwamna Zulum hari

Aminu Mallam wanda aka fi sani da Baderi shine ake zargi da garkuwa da mutane. An kamasa ne a kauyen Sabon gayan.

A ranar 2 ga watan Satumba ne, atisayen 'Thunder Strike' daga sojin runduna ta daya suka kai samame sansanin masu garkuwa da mutane dake kauyukan Ligari da Sabon gayan. Bayan kwanaki kadan ne da kai samamen ne aka gano shanun a yankin Ligari.

Rundunar ta ce ta samu bayanan sirri daban-daban wanda hakan ne yasa ta kai samamen.

Sojin sun bayyana cewa abin takaicin da suka gano shine barayin shanun kan yi hayar matasan da ba su ji ba, ba su gani ba don kiwon dabbobin da suka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel