Babban rashi: Buhari ya yi alhinin mutuwar Robert Mugabe

Babban rashi: Buhari ya yi alhinin mutuwar Robert Mugabe

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, ROBERT Mugabe, wanda ya rasu a ranar Juma’a yana dan shekara 95 a duniya, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buhari ya yi ta’aziyyar mutuwar Mugabe ne ta bakin kaakakinsa, Mista Femi Adesina, inda ya taya iyalai, yan uwa da abokan arzikin Mugabe jimamin rashin da suka yi.

KU KARANTA: Dalilin da yasa Sarkin Kano da Gwamna El-Rufai suka tafi kasar Afirka ta kudu

Shugaban kasa Buhari yace Mugabe ne ya jagoranci yakin neman yancin kasar Zimbabwe daga mulkin mallaka na turawan yamma, kuma ya yi yawancin rayuwarsa yana bauta ma yan kasarsa.

Buhari yace tarihi ba zai manta da sadaukarwar da Mugabe ya yi ma al’ummarsa ba, musamman gwagwarmayar da yayi don ceton jama’ansa daga takunkumin tattalin arziki da kuma siyasa.

Daga karshe Buhari ya yi fatan Allah Ya kyautata makwancin ruhin Mugabe, tare da baiwa yan uwansa hakurin rashin jigonsu.

Shi dai Mugabe ya rasu ne a wani babban asibitin kasar Singapore inda ya kwashe tsawon lokaci yana jinya a can, sai dai gwamnatin kasar Zimbabwe bata bayyana irin cutar dake damunsa ba.

Marigayi Robert Mugabe ya kwashe tsawon shekaru 37 yana mulkar kasar Zimbabwe tun bayan samun yancin kasar daga hannun turawa a shekarar 1980, har sai a wata Nuwambar shekarar 2017 ne Sojoji suka hambarar da gwamnatinsa.

Shima shugaban kasar Zimbabwe da ya gaji Mugabe, Emmerson Mnangwagwa ya bayyana alhinin mutuwar maigidan nasa, inda yace:

“Ina bakin cikin sanar daku mutuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe. Mugabe jagoran gwagwarmayan neman yanci ne, kuma mutum wanda ya sadaukar da ransa wajen cigaban jama’ansa, ba zamu taba mantawa da gudunmuwar daya baiwa kasar nan ba.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel