An fasa kwai akan dalilin da yasa yan Najeriya basa biyan haraji

An fasa kwai akan dalilin da yasa yan Najeriya basa biyan haraji

Rahotanni sun nuna cewa sama da kaso 81 cikin 100 na manyan da biyan haraji ya hau kansu da kasuwanci a Najeriya basa biyan haraji daga kudaden shigarsu, kungiyar taron tattalin arziki na Najeriya wato Nigeria Economic Summit Group (NESG) ta bayyana hakan.

Daraktan bincike na manufar NESG, Tayo Oyedele, ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 65 ga watan Satumba lokacin da ya jagoranci wata tawaga don ziyartan Darakta Janar na kungiyar gwamnonin Najeriya, Mista Asishana Bayo kauru a Abuja, jaridar Daily Trust ruwaito.

Wani jawabi dauke da sa hannun kakakin kungiyar, Abdulrazaque Bello-Barkindo, yace Oyedele tare da rakiyar Shugabar FFR, Dr Sarah Alade, sun yi amfani da dammar wajen fallasa halin da harajin ke ciki ga gwamnonin.

An kuma kai ziyarar ne domin neman goyon bayansu wajen gyara wannan gibi da ke hana ksar kdaden shigar ta, inji sanawar.

Oyedele ya koka akan halin yan Najeriya wajen biyan haraji, inda ya kara da cewa kididdiga ya nuna cewa akwai masu biyan haraji miiyan 20 da aka yi wa rijista a kasar.

Yace wannan adadin kadanne idan aka kwatanta da kasar da ke da yawan mutane kusan miliyan 200.

Yayinda yake bayani akan manufa da dalilin da yasa kasar ke samun karancin haraji, Shugaban na NESG a bayyana cewa kusan kaso 85% na wadanda ke ganin ba dole bane biyan gwamnati haraji da gangan sukan biya hakan ga mutane masu zaman kansu.

KU KARANTA KUMA: Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Wani matashi dan shekara 16 ya nutse a ruwa a Kano

Ya daura alhakin haka ga rashin yarda da mutane ke dashi idan aka zo fannin biyan haraji ga gwamnin da bata aiwatar da abunda mutane ke tsammani daga gare ta.

A nashi bangaren Darakta Janar na kungiyar gwamnonin kasar, Asishan Bayo Okauru, yace lamarin babban annoba ne da ya zama dole ayi gaggawan magane shi. Ya yi godiya ga kungiyar NESG da suka sana da kungiar abunda ake ciki ta fannin haraji.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel