Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Wani matashi dan shekara 16 ya nutse a ruwa a Kano

Innalillahi wa’inna illaihi raji’un: Wani matashi dan shekara 16 ya nutse a ruwa a Kano

Wani matashin yaro dan shekara 16 mai suna Shahid Lawal, ya nutse a cikin ruwa yayinda yake wanka a ikin wani kogo a Bacharawa Ramin Kasa, karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano.

Wannan bayani na kunshe a wani jawabi dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Mista Saidu Mohammed, a ranar Juma’a, 6 ga watan Satumba.

Mohammed ya bayyana cewa lamarin ya afku ne a yammacin ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, lokacin da marigayin ya je wanka.

“Mun samu wani kira mai cike da damuwa daga Rabiu Nasiru da misalin karfe 6:23 na yamma cewa an ga gawar Lawal yana yawo a saman kogin.

“Da muka samu bayanin, sai muka yi gaggawan tura tawagar ceto zuwa wajen da lamarin ya faru da misalin karfe 6:34 a yamma.”

KU KARANTA KUMA: Najeriya ta sanar da ranar da za ta fara kwashe yan kasarta daga kasar Afrika ta Kudu

Har yanzu ana kan binciken abunda ya haddasa lamarin.

“An gano Lawal a mace sannan aka mika shi zuwa ga mai unguwar Bachirawa Gabas, Alhaji Rabiu Bala,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel