Najeriya ta sanar da ranar da za ta fara kwashe yan kasarta daga kasar Afrika ta Kudu

Najeriya ta sanar da ranar da za ta fara kwashe yan kasarta daga kasar Afrika ta Kudu

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewar Najeriya za ta fara kwashe al’umman kasarta daga kasar Afrika ta Kudu da ke dama da rikici a ranar 7 ga watan Satumba, 2019.

Ma’aikatar harkokin waje ce ta fitar da sanarwar, sannan kuma ta yaba ma Cif Allen Onyema, wanda ya bayar da gudunmawar jirginsa domin kwaso su.

Ma’aikatar ta kuma saki lambobi waya guda tara ga wadanda ke da ra’ayin dawowa Najeriya.

A cewar sanarwar, yan Najeriya da ke da ra’ayin dawwa kasar su gabatar da cikakken sunayensu, kauye, karamar hukuma da kuma jiharsu, adireshin su da kuma magajinsu.

Hakazalika za su samar da lambobin wayarsu, kwafi na fasfot dinsu ko kuma katin shaidarsu da kuma hoton fasfot guda biyu.

Ma’aikatar ta kuma kara da cewa duk dan Najeriya da bai da katin shaida ma na iya shiga cikin jerin masu dawowa.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Buhari da Gbajabiamila sun yi ganawar sirri a Aso Rock

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ma’aikatar harkokin kasashen wajen Najeriya ta sanar da al’ummar kasar cewa jiragen Air Peace za su debo ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudun zuwa gida Najeriya saboda kisan gillan da ake yi masu a can kasar.

Mai kamfanin jiragen Air Peace Cif Allen Onyema ya dauki nauyin tura jiragensa domin yin wannan aiki na dawo da ‘yan Najeriya gida kyauta.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel