Robert Mugabe: Maganganu 10 masu tasiri da yayi a lokacin rayuwarsa

Robert Mugabe: Maganganu 10 masu tasiri da yayi a lokacin rayuwarsa

Kasancewar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya mutu ya na da shekara 95 a duniya, akwai wasu maganganu 10 da yayi a lokacin rayuwarsa wadanda suka yi tasiri mai girman gaske.

A lokacin rayuwarsa a matsayin shugaban kasar Zimbabwe, Mugabe yayi maganganu sosai ba a kan siyasa kadai ba hadda auren jinsi, tattalin arziki, shugaban kasar Amurka da dai sauransu.

KU KARANTA:Abubuwa 16 da baku sani ba game da marigayi Mugabe

Ga wadansu jerin maganganunsa 13 da gidan talbijin na Aljazeera ta ruwaito ta fitar:

1. A shekarar 1962 tsohon shugaban kasan yayi magana a kan yadda aka kasafta nahiyar Afirka a garin Salisbury. “Ya zama wajibi Afirka ta koma yadda take a da a matsayin tsintsiya madaurinki daya.” Inji Mugabe.

2. A taron jam’iyyarsa ta ZANU-PF, Mugabe ya roki farar fata mazauna kasar da cewa su cigaba da zama. “Ku cigaba da zama damu domin mu gina kasa guda cikin hadin kai da zaman lafiya.” Inji shi.

3. A wani lokaci cikin shekarar 2008 da aka matsa masa lamba kan cewa lallai sai ya sauka daga bisa mulki, sai ya ce: “Ubangijin da ya bani wannan mulkin ne kadai zai iya sauke ni, ba MDC ko turawan Burtaniya ba. Allah ne kadai zai iya sauke ni.”

4. Mugabe a lokacin taronsa na kamfe a shekarar 2002 ya ce turawa makiyan kasar Zimbabwe ne. “Dole jam’iyyarmu za ta cigaba da jefa tsoro cikin zukatan turawa saboda su din makiyanmu ne na hakika.” A cewarsa.

5. Tsohon shugaban Zimbabwe yayi magana sosai gameda auren jinsi inda ya hakikance kwarai da gaske a kan cewa wannan abin ba al’adar nahiyar Afirka bane. “Muna tambayar turawan yamma ko a haka aka samar da su. Namiji ya bi namiji, mace ta bi mace, sam ba zamu aminta da wannan ba, saboda ko dabba ya san mace.” Inji Mugabe.

6. Haka kuma ya kara da cewa: “Ko kadan ba zamu aminta da abubuwa da suka ci karo da al’adunmu ba a matsayinmu na bakar fata ‘yan nahiyar Afirka.”

7. Tsohon shugaban kasan yayi magana mai ban dariya gameda Burtaniya a shekarar 2013. “Burtaniya akwai sanyi sosai, babu dadin zaman sannan cike take da kananan gidaje.”

8. A shekarar 2002 a kasar Afirka ta Kudu, Mugabe ya yiwa tsohon Firai ministan Burtaniya Tony Blair wankin babban bargo inda ya ce: “Mun gwabza a yanki ta hanyar nemawa kasarmu ‘yanci, a don haka Blair ka ji da kasarka ta Ingila ka barmu da tamu kasar.”

9. Mugabe yayi magana dangane da tsohon shugaban Amurka Bush a shekarar 2017. “Akwai bukatar Bush ya koma ya duba tarihi. A matsayinsa na shugaban kasa da kuma dan Amurka fafutukar cigaba yake ta yi.”

10. “ Tunda dai har Obama ya aminta da auren jinsi a kasarsa, kuma yana so mu ma mu amince da shi. In har zai yadda zan taho Amurka in nemi aurensa.” A cewar Mugabe game da auren jinsi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel