EFCC ta kama jami’an karamar hukuma guda 4 da cin albashin ma’aikata a Sakkwato

EFCC ta kama jami’an karamar hukuma guda 4 da cin albashin ma’aikata a Sakkwato

Hukumar EFCC reshen jahar Sakkwato ta samu nasarar kama wasu jami’an karamar hukumar Sabon Birni guda 4 da laifin danne albashin ma’aikatun hukumar su 114, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban EFCC na wannan shiyyar, Abdullahi Lawal ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 5 ga watan Satumba, inda yace daga cikin jami’an da suka kama har da sakataren ilimi na karamar hukumar, Ishaka Abdullahi da mataimakinsa Abdullahi Idris.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Zamfara za ta gina katafaren gidan masaukin baki na biliyan 9

Sauran sun hada da jami’in biyan kudi na karamar hukumar, Abdullahi Dadi da kuma jami’in kula da shige da ficen kudi na karamar hukumar Sabon Birni, Idris Wambai.

Shugaban Lawal ya bayyana cewa sun kama mutanen 4 ne bayan samun takardar korafi daga malaman makarantun firamari na karamar hukumar su 114, inda suka bayyana cewa tsawon watanni da dama basa samun albshi.

“Mun kaddamar da bincike cikin maganar, wanda hakan ya kaimu ga bankado wasu muhimman takardu da suka sabbaba daukan wannan mataki, mun gano cewa tun shekarar 2013 karamar hukumar Sabon Birni tana da jerin sunayen ma’aikatan bogi 208 da take biyansu albashi duk wata.

“Yadda suke yi shi ne sai su dinga zaftarar albashin halastattun ma’aikatun karamar hukumar suna biyan wadancan ma’aikatu na bogi, ma’ana suna kwashe kudaden jama’a.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban na EFCC ya bayyana cewa sun kama wani dan damfara mai suna Muzakkir Muhammad ya yi kaurin suna a jahar Sakkwato wajen buga takardun kudi na bogi.

Daga karshe yace zasu gurfanar da mutanen dukansu gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel